An ‘sace’ ‘yan makaranta 81 a Yammacin Kamaru

News

An sace mutane da dama, cikin su har da yara a wata makaranta da ke birnin Bamenda na Jamhuriyar Kamaru.

Kamfanonin dillancin labarai sun ambato wasu majiyoyi na gwamnati da sojin kasar da ba sa so a bayyana sunayensu sun ce an sace a kalla mutum 79.

Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa ‘yan bindiga ne suka sace mutanen ranar Litinin da safe.

Da ma dai yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru na fama da rikice-rikicen ‘yan a-ware a shekarun baya-bayan nan.

An ‘kashe jami’an tsaro 84’ a Kamaru
Yadda Paul Biya ya sake lashe zaben shugaban Kamaru
‘Yan bindiga, wadanda suke yunkurin ganin yankunan da ke magana da turancin Ingilishi sun balle daga kasar, sun sha yin kiraye-kiraye a kaurace wa makarantu.

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin sace mutanen.

Kungiyoyin ‘yan a-ware
‘Yan a-waren, wadanda ke son kafa sabon yankin Ambazonia, sun soma fafituka ne a 2017 bayan jami’an tsaro sun yi dirar mikiya kan kungiyoyin zanga-zanga, wadanda lauyoyi da malaman makarantu ke jagoranta bisa zargin gazawar gwamnati wurin bayar da cikakkiyar kulawa ga yankunan masu magana da turancin Ingilishi da ke Arewa maso Yamma da Kudu Maso Yammacin kasar.

An zargi gwamnati da ba da mukamai masu tsoka ga mutanen da suka samu horo daga yankunan da ake magana da ke magana da turancin Faranshi wajen harkokin shari’a da malanta, suna danne masu magana da turancin Ingilishi wadanda su ne kashi 20 cikin 100 na al’ummar kasar.

A kwanakin baya ne Shugaba Paul Biya, wanda ke kan mulki tun 1982, ya sake lashe zabe karo na bakwai da fiye da kashi 70 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Amma ‘yan hamayya sun yi zargin an yi magudin zabe, ko da yake yunkurin d aka yi na ganin an soke zaben ya ci tura.

@www.bbc.com

Leave a Reply

Your email address will not be published.