Rikicin ‘yan Shi’a: Sojoji sun kafa hujja da Trump kan harbin ‘yan Shi’a

Reports
People stand next to a police car that has set alightHakkin mallakar hotoAFP
Image captionJami’an tsaro sun ce rikicin ya fara ne bayan da masu zanga-zangar suka yi kokarin karbe iko da wani shingen bincike

Rundunar sojin Najeriya ta kafa hujja kan bude wa ‘yan Shi’a wuta da wani faifan bidiyon na Shugaban Amurka Donald Trump, wanda a ciki shugaban yake cewa sojoji za su iya amfani da karfi kan baki ‘yan ci rani da ke jifansu da duwatsu.

“Idan suka yi jifa da duwatsu… ku dauka sun yi da bindiga ne,” in ji Mista Trump a wani faifan bidiyo.

Jami’an tsaron Najeriya sun kama mabiya Shi’a 400 bayan wani mummunan artabu na tsawon kwanaki a Abuja.

  • Kalli hotunan artabun ‘yan Shi’a da sojoji a Abuja
  • Me Amurka ta ce kan rikicin ‘yan Shi’a a Abuja?
  • Jonathan ya soki Buhari kan ci gaba da tsare Zakzaky

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki sojojin kasar da kashe ‘yan Shi’a, inda ta ce zanga-zangar ta lumana ce.

Sai dai mai magana da yawun sojojin kasar Burgediya Janar John Agim ya ce sun amfani da harsasai masu rai ne ga masu zanga-zanga saboda suna dauke da makamai.

Ya ce: “Wannan ne abin da Mista Trump yake magana a kai.”

Shafin Twitter na rundunar sojin kasar ta wallafa bidiyon da rubutu kamar haka: “kalla kuma ga yadda hujjar ta fito”.

Kakakin sojin ya ce sun wallafa bidiyon ne saboda mayar da martani ga rahoton kungiyoyin kare hakkin dan Adam da suke cewa sojoji sun yi amfani da makami kan ‘yan Shi’a masu zanga-zanga.

Sai dai rundunar sojin ba ta yi magana game da sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya fitar ba, inda Amurka ta bukaci “gudanar da bincike da hukunta masu laifi a rikicin.”

Ba a san adadin ‘yan Shi’an da sojojin kasar suka kashe a Abuja lokacin artabun da aka kwashe tsawon kwanaki ana yi a birnin ba.

Sojoji sun ce mutum shida ne suka rasa rayukansu, amma ‘yan Shi’a sun ce adadin yana da yawa sosai, sai kungiyar Amnestry ta ce adadin ya kai 45.

Rikicin ya fara ne a lokacin da ‘yan Shi’ar suka fara tattaki Arbaeen na shekara-shekara a Abuja – wato tarukan tunawa da kisan jikan Manzon Allah (SAW).

‘Yan Shi’an suna neman sakin jagoransu ne Sheikh ibrahim Zakzaky wanda ake tsare da shi kimanin shekara uku ke nan, bayan wani rikici da kungiyar ta yi da sojoji a Zaria.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *