Saudiya ta gaskata mutuwar Khashoggi

Bayan mako biyu da aka kwashe Saudiya na musanta zargin da ake mata, a karshe ta fito ta amince cewa dan jaridar nan Jamal Khashoggi kashe shi aka yi a cikin ofishin jakadancinta da ke birnin Santanbul na Turkiyya.

Tashar Talabijin Saudiya ta ce Mista Khashoggi ya mutu ne bayan barkewar fada a ofishin jakadancinta- sai dai ba ta bayyana abin da ta yi da gawarsa ba.

Saudiya ta fuskanci matsin lambar diflomasiya kan ta yi bayyani yadda aka yi Mista Khashoggi ya yi batan dabo, bayan jami’an Turkiyya sun tabbatar an kashe shi a cikin ofishin jakadancinta, sannan aka yi gunduwa-gunduwa da shi.

Shugaba Trump na Amurka ya bayyana matakin Saudiya na bayyana abinda ya faru da Jamal Kashoggi a matsayin matakin farko mai kyau, kana ya nuna gamsuwarsa da bayananta inda ya ce akwai sahihanci a ciki.

Kafar talbijin kasar ta ce tuni aka kori mataimakin shugaban hukumar leken asirin kasar ta Saudia da kuma wani babban mai bayar da shawara ga yarima mai jiran gado a kan wannan batu.

Wannan ne dai karon farko da masarautar Saudi Arabiyan ta amince da cewa Jamal Kashoggi ya mutu.

‘Turkiyya na da shaida a kan kisan Khashoggi’
Wane ne Jamal Khashoggi? Dan jaridar Saudiyyan da ya yi batan dabo
Rahotanni sun ce sarki Salman ya bayar da umarnin a kafa wani kwamiti na ministoci karkashin jagorancin yarima mai jiran gado domin yin garan bawul a ayyukan hukumar leken asirin kasar.

Tun a ranar 2 ga watan da muke ciki ne ba a sake jin duriyar Mista Kashoggi ba, bayan ya shiga ofshin jakadancin Saudiya da ke Turkiyya domin karbar wasu takardu da za su bashi damar aurar budurwa.

Rahotannin daga Saudiyar a kan mutuwar Jamal ya zo ne jim kadan bayan sarki Salman ya yi waya da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a kan batun.

Wata sanarwa daga mai shigar da kara na kasar Saudiya ta ce fada ya barke ne tsakanin Mista Kashoggi da kuma wasu mutane da ya hadu da su a cikin ofishin jakadancin lamarin da ya yi sanadiyyar ajalinsa a wajen.

Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma tuni ‘yan sanda a Turkiyya suka fadada bincike domin gano gawar Mista Kashoggi.

Sakatare janar ma Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya damu matuka da wannan abu da Saudiya ta fada, inda kuma ya jaddada bukatar da ke akwai na hukunta duk wanda aka samu da hannu a kisan dan jaridar.

@www.bbc.com

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *