Mutum 55 aka kashe a rikicin Kaduna – ‘Yan sanda

Kimanin mutum 55 ne suka rasa rayukansu bayan wani rikici da ya barke a jihar Kaduna, kamar yadda rundunar ‘yan sanda a jihar ta bayyana.

A ranar Juma’a ne gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garin Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru ta Kudancin jihar bayan wani rikici da ya barke a garin.

“Mun kama kimanin mutum 22 da muke zargi suna da hannu a tada zaune tsayen kuma zuwa yanzu tsaro ya inganta a yankin,” in ji rundunar ‘yan sandan.

Sai dai akwai wadansu rahotanni da ke cewa adadin mutanen da suka mutu ya zarta hakan.

Rikicin dai ya barke ne ranar Alhamis, lokacin da kasuwar garin ke ci kuma ta cika makil da jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wasu jihohi.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya shaida wa BBC cewa “muna tsaka da cin kasuwa kawai sai wasu matasa da dama sun yi kaurin suna wajen ta da irin wadannan fituntunu, suka fado cikin jama’a da doke-doke suna karya rumfuna suna jidar kayan jama’a.”

Ya bayyana cewa mutane da yawa sun rasa rayukansu, sai dai bai san adadinsu ba.

Haka kuma, ya ce rikicin ya kai har cikin dare ana yi kuma sai da safe ne jami’an tsaro suka fara aikin tattaro gawarwaki a garin.

“Gaskiya an kona gidajen jama’a, da rumfunan kasuwa kafin jami’an tsaro su shigo cikin garin” a cewarsa.

Kaduna: ‘Za mu hukunta masu haddasa rikici’
Gwamnatin Nigeria ta bukaci karfafa tsaro kan rikicin Kaduna
A baya dai an sha samun rikice-rikicen kabilanci da addini a garin Kasuwar Magani.

A wannan karon ma, rahotanni na cewa rikicin ba ya rasa nasaba da kabilanci da addini.

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kadunan ta bakin sakatarenta Sunday Ibrahim, ta nuna rashin jin dadinta da sake barkewar rikici a garin.

Ya ce “ya kamata gwamnati ta san cewa, wadanda aka kama da sa hannunsu a wannan abu kada a sake su, don wani lokaci idan aka kama mutane ba a yi musu hukunci ba sai aka sake su shi yake haddasa irin wannan.”

Ya ce kamata ya yi a shigar da shugabannin addinai a cikin duk wani kokari na kawo karshen rigingimun addini a jihar Kaduna.

Jihar Kaduna dai na daya daga jihohin arewacin Najeriya da ke fama da rikicin addini da kabilanci.

@www.bbc.com

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *