Fursuna mai shekara 100 na son Najeriya ta yi mai afuwa

Paul and Celestine EgbunucheHakkin mallakar hotoGLOBAL SOCIETY FOR ANTI-CORRUPTION
Image captionPaul da Celestine Egbunuche sun kasance a tsare tsawon shekara 18 kuma sun yi shekara hudu suna jiran hukuncin kisa

Wani fursuna da ke jiran a zartar masa da hukuncin kisa wanda aka yi wa lakabi da “fursunan da ya fi tsufa a Najeriya” yana neman a yi masa afuwa.

Fursunan mai suna Celestine Egbunuche, mai shekara 100, ya shafe shekara 18 a tsare bayan an same shi da laifin kisan gilla.

Ana tsare ne da Mista Celestine tare da dansa Paul a babban gidan yarin jihar Enugu a kudu-maso-gabashin Najeriya.

Ana tuhumar Paul mai shekara 41 da mahaifinsa ne da laifin daukar hayar wasu mutane wadanda suka sace wani mutum kuma daga baya suka kashe shi, bayan wata takaddama kan filaye a jihar Imo.

An fara tsare su a shekarar 2000 kafin a yanke musu hukuncin kisa a shekarar 2014.

  • An yanke wa Musulmi 75 hukuncin kisa a Masar
  • An rage yanke hukuncin kisa – Amnesty
  • Kotu ta yanke wa sojin Najeriya hukuncin kisa

Sai dai yana da wuya a iya gane iyalan mutumin da aka kashe – hatta jami’an gidan yarin sun kasa dacen samun dangin mamacin.

Wani jami’in gidan yarin ya ce Mista Celestine ba ya iya magana kuma ba ya iya fahimtar abin da ke faruwa a kusa da shi.

“Idan ka tambaye shi abin da ke faruwa a kusa da shi, sai yai maka maganar wani abu daban. Likitoci sun ce min saboda shekarunsa ya koma kamar wani karamin yaro.”

“Akwai lokacin da yake tambayata cewa: ‘Wadannan mutanen (fursinoni ke nan), me suke yi a nan?”

Prisoners in a prison in Enugu, Nigeria, pictured in 2009
Image captionAkwai fursinonin Najeriya da dama wadanda suke jiran shari’a

Paul ya ce yana da wuya ya yi nesa da mahaifinsa yanzu; shi ne babban mai kula da shi tun da rashin lafiyarsa ta kara ta’azzara.

Matsalolin sun hada da ciwon siga da matsalar gani kuma Paul yana bakin kokarinsa wajen ganin ya taimaka masa a kodayaushe.

“Ina kula da shi kawai ta hanyar ba shi abinci da danyen agada, kuma jami’an gidan yarin suna kawo masa magani.”

Hoton zagayowar ranar haihuwa

Uba da dan suna zaune ne a gidan kurku guda wanda aka raba su da sauran fursinoni gidan yarin.

“Idan na tashi da safe, ina dafa ruwan zafi, na yi masa wanka,” in ji Paul.

“Daga nan sai na canja masa kaya, na dafa masa abinci. Idan an bude dakin da muke zaune ciki, sai na fito da shi waje don rana ta taba shi.”

“A kodayaushe ina tare da shi, muna magana, muna wasa.”

Paul ya ce wadansu fursunoni suna taimaka masa wajen taimakon mahaifinsa, kuma galibinsu suna so a yi wa mahaifin nasa afuwa.

Bayan mahaifinsa ya cika shekara 100 a ranar 4 ga watan Agusta sun yi tunanin cewa wannan lokacin ne ya dace a sallame shi.

Wani hoto da Paul ya dauka tare mahaifinsa wanda aka yada a watan Agusta, inda wata jarida ta yi labarin yadda ya cika shekara 100 a gidan yari.

Daga nan sai aka fara tafka muhawara a kan tsawon lokacin da ‘yan Najeriya za su kwafe suna jiran hukuncin kisa.

Alkalunma daga hukumar da ke kula da gidajen yarin kasar sun ce mutane fiye da 2,000 ne a ka zartar wa da hukuncin kisa a kasar, galibinsu kuma sun shafe shekaru suna jiran haka.

Ba a cika zartar da hukuncin kisa a Najeriya ba.

Tsakanin shekarar 2007 zuwa 2017 mutum bakwai ne kawai aka zartar wa hukuncin kisa a kasar, kamar yadda kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ruwaito.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *