Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudin zaben 2019

Sanata Bukola SarakiHakkin mallakar hotoTWITTER/BUKOLA SARAKI
Image captionMajalisar ta kara naira biliyan 45.5 a kan naira biliyan 189 da kwamitin majalisar kan INEC ta gabatar da farko

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudi na naira biliyan 189 wanda hukumar zabe za ta yi amfani da shi don ayyukan zaben da za a gudanar a shekarar 2019.

Sai dai majalisar dattawan ba ta amince da kasafin kudin jami’an tsaro da Shugaba Muhammadu Buhari ya mika masu ranar Laraba.

Sanata Ahmad Lawan ya shaida wa BBC cewa “a yanzu kwamitocin majalisar na kudi da na kasafin kudi na aiki kan tantance kasafin kudi da Shugaba Buhari ya bukaci a bai wa jami’an tsaro don amfani da shi a zaben badi.”

Ya kuma ce suna sa rai zuwa mako mai zuwa ne majalisar za ta amince da kasafin kudin jami’an tsaron.

  • Shin me Buhari ya fada wa shugabannin Majalisa?
  • ‘Yanzu PDP ta fi APC karfi a majalisar dattawa’

Haka kuma, majalisar ta kara naira biliyan 45.5 a kan naira biliyan 189 da kwamitin majalisar kan INEC ta gabatar da farko.

Hakan ya sa gaba daya kudin da majalisar ta amince zuwa naira biliyan 234.5.

Majalisar dai ta amince da kasafin kudin ne bayan da shugaban kwamitin kasafin kudi, Danjuma Goje ya mika rahoton da kwamitin nasa ya hada bayan duba wasikar da Shugaba Buhari ya aika wa majalisar.

Ranar Laraba ne shugaban ya rubuta wa majalisar dattawan, inda ya bukaci su amince da naira biliyan 242 kamar yadda hukumar INEC da hukumomin tsaro suka bukata don gudanar da zabukan 2019.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *