Shin ko Obasanjo ya ce a zabi Buhari, kada a zabi Atiku a 2019?

Buhari da Atiku
Image captionShugaba Muhammadu Buhari (daga hagu) da Alhaji Atiku Abubakar ne za su fafata a babban zaben Najeriya 2019

Tun bayan da babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta tsayar da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, jama’a suke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu game da dan siyasar musamman a kafofin sada zumunta a kasar.

Yayin da wadansu suke ganin tsohon mataimakin shugaban kasar zai iya doke Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, wasu suna ganin hakan ba mai yiwu ba ne.

Wannan batun shi ne abin da ya mamaye shafukan sada zumunta a Najeriya tun bayan da manyan jam’iyyun kasar biyu suka sanar da sunayen wadannan ‘yan siyasan.

Jama’a sun rika yada labarai musamman game da Alhaji Atiku Abubakar wadanda ba sahihai ba ne, ciki har da wadanda ake ikirarin cewa wai sun fito ne daga kafar yada labarai ta BBC.

Da gaske ne Obasanjo ya ce a zabi Buhari, kuma kada a zabi Atiku a 2019?

FacebookHakkin mallakar hotoFACEBOOK/ABUBAKAR SADIQ

An rika yada labaran karya a kafofin sada zumunta inda ake cewa tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci ‘yan kasar da su zabi Shugaba Buhari a zaben 2019, kuma Atiku ba zai taba yin shugabancin kasar ba.

Atiku, wanda ya yi wa Obasanjo mataimakin shugaban kasa tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007, bai taba samun goyon bayansa ba a fafutikar da ya sha yi a baya na neman takarar shugabancin kasar.

Kodayake Shugaba Buhari ya samu goyon bayan Mista Obasanjo a lokacin da ya lashe zaben 2015, amma daga bisani a bana, ya bayyana cewa ba ya goyon bayan tazarcen shugaban.

BBC ba ta yi wata hira da Mista Obasanjo ba kan zaben 2019, hakazalika babu wani labari mai kama da wannan da kafar yada labaran ta ruwaito.

Shin Atiku ya kai ziyara Amurka har ya gana da Trump?

A wata hira da BBC ta yi da Alhaji Atiku Abubakar game da neman takararsa a zaben 2019 wanda aka yi da shi a ofishinmu na Landan a bana.

Editan sashen Hausa Jimeh Saleh ya tambaye shi dalilin da ya hana shi zuwa kasar Amurka, inda Atikun ya ce bai san dalilin da ya sa kasar ta hana shi Biza ba.

Shi ma wannan batun ya ba da wata kafa ta yada wasu labaran kanzon kurege a kafofin sada zumunta.

An rika wallafa wani hoton boge a shafin sada zumunta inda ake ikirarin nuna dan siyasar yana gaisawa da Shugaba Donald Trump a gaban fadar White House bayan taron manema labarai.

Ko jikar Atiku ta ce Sai Buhari?

Hakazalika an rika wallafa wani sakon boge wanda aka ce ya fito ne daga shafin Twitter na Alhaji Atiku, inda ake cewa wata jikarsa ta ce masa “Najeriya Sai Buhari” bayan da ya koma gida bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.

Wannan ma labarin kanzon kurege ne don shafin da ya wallafa wannan sako a Twitter ba na dan siyasar ba ne.

Atiku ya wallafa wannan sakon: “A karshe na koma gida bayan zaben fidda gwani. Jikata ta yi mun maraba. Kuma yanzu ina kewaya gidan da ita rike da balan-balan (mai dauke da rubutun) Sai Atiku a 2019,” in ji shi.

Bambancin shafin bogen da sahihin shafin Atiku Abubakar

  • Sunan shafin @The_Atiku, maimakon nasa na aihini mai suna @atiku
  • An bude shi ne a watan Oktobar shekarar 2018, dan siyasar ya bude na shi sahfin a shekarar 2010
  • Yana da mabiya 261 ne kawai, maimakon mabiya miliyan daya da rabi da sahihin shafin dan siyasar yake da su.
Presentational grey line

Menene labaran karya?

Sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane.

Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba.

Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu.

A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar-dar.

  • Obasanjo bai isa ya hana ni komai ba – Atiku Abubakar
  • Yadda labaran karya ke ruruta rikicin makiyaya da manoma
  • Hanyar gane labaran karya da ake yadawa a intanet
Presentational grey line

Irin wadannan labaran karya kan haifar da illoli masu yawa, kamar tayar da fitina, da kulla kiyayya tsakanin al’umma da kuma yada bayanan da ba su da tushe.

Binciken da BBC ta yi a kwanakin baya ya gano cewa labaran karya na sahun gaba wurin yada rikicin da ake fama da shi a Najeriya tsakanin makiyaya da manoma.

Hakan ne kuma ya sa ma’aikatar sadarwa ta kasar kaddamar da wani shiri na musamman domin yaki da wannan dabi’a, wacce ke kara samun gindin zama a kasar, musamman a shafukan sada zumunta.

Yadda ake gane labaran karya

Akwai yiwuwar cigaba da samun labaran karya kan wannan rikici, musamman a lokacin da ake tunkarar zaban shugaban kasa a badi.

Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana’ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Rikici na baya bayan nan shine na jihar FilatoHakkin mallakar hotoAFP
Image captionMutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa

Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa.

Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu.

Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa. T

abbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na’urar da aka yi amfani da ita.

Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani. Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu yake.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *