APC ba ta yi adalci ba a zabukan fitar da gwani — Aisha Buhari

Politics
Aisha BuhariHakkin mallakar hotoTWITTER/@AISHAMBUHARI

Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta soki jam’iyya mai mulki APC dangane da yadda ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta a 2018.

Aisha Buhari, wadda ta rubuta a shafinta na Instagram cewa ‘ Abin takaici ne wasu ‘yan takara sun yi amfanin da kudin guminsu sun sayi fom din takara, sannan an tantance su, kana sun yi yakin neman zabe iya karfinsu, amma kuma an cire sunayensu a ranar zabe.’

Uwargidan shugaban Najeriyar, ta ce ‘ Babban abin takaicin shi ne yadda wadannan ‘yan takara suka sayi fom din a kan kudi mai yawa’.

Ta ce ‘ Da yawa daga cikin wasu ‘yan takarar kuma har yanzu suna dakon sakamakon zaben, wanda sanin kowa ne cewa tuni aka ba wa wasu takarar shi yasa ake jan kafa wajen fadin sakamakon.’

Aisha Buhari ta ce, Makasudin kafa jam’iyyar APC shi ne don a samar da sauyi nagari, amma bain takaicin shi ne yadda wannan al’amari ya faru a karkashin jagorancin Adams Oshimole, mutumin da aka sani da nuna damuwa da kuma kokarin kwatowa talakawa ‘yancinsu.

Uwargidan shugaban Najeriyar ta ce, wannan al”amari ya sa mutum ba shi da zabi illa ya nesantar da kansa daga wannan rashin adalcin ya kuma yi magana a madadin wadanda aka tauye musu hakkinsu.

Ta ce yana da muhimmanci al’umma su tashi tsaye wajen ganin cewa ba a tauye musu hakkinsu ba.

Sai dai wasu na ganin Aisha Buhari, ta yi wadannan kalamai ne saboda rashin samun tikitin takarar kujerar gwamna a jihar Adamawa a jam’iyyar APC da uwanta ya yi.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *