Cristiano Ronaldo ya musanta zargin yi wa wata mata fyade

Cristiano Ronaldo. Photo: 29 September 2018Hakkin mallakar hotoALLSPORT/GETTY IMAGES
Image captionShahararren dan wasan Portugal din yanzu yana wasa ne a kungiyar Juventus ta Italiya

Dan wasan kungiyar Juventus Cristiano Ronaldo ya musanta zargin da wata mata Ba’amurkiya ta yi masa cewa ya taba yi mata fyade a shekarar 2009.

Tsohon dan kwallon kungiyar Real Madrid din ya ce “labarin kanzon kurege ne.”

A wani faifan bidiyo a shafin Instagram, Ronaldo ya ce: “Suna so ne su tallata kansu ta hanyar amfani da sunana. Wannan abu ne da aka saba yi.”

Lauyoyin shahararren dan wasan sun ce za su yi karar mujallar kasar Jamus Der Spiegel wadda ta fara ruwaito labarin.

Mujallar ta ruwaito matar mai suna, Kathryn Mayorga, tana cewa shahararren dan wasan, mai shekara 33, ya yi mata fyade a wani otel da ke birnin Las Vegas na kasar Amurka.

  • Rayuwar kwallon Ronaldo cikin hotuna
  • Ronaldo na bacci zai rika karbar miliyan 12 a Juventus
  • Kwallon Ronaldo ta girgiza duniyar tamaula

Har ila yau mujallar ta ce Mis Mayorga, mai shekara 34, ta kai kara a wani ofishin ‘yan sanda da ke Las Vegas jim kadan bayan faruwar al’amarin.

A shekarar 2010, matar ta ce sun cimma yarjejeniyar wajen kotu da Ronaldo, inda ya amince zai biyata dala 375,000, idan ta ki bayyana wa duniya abiin da ya faru a tsakaninsu.

Sai dai a wata sanarwa da lauyan dan wasan Christian Schertz ya fitar ta ce: “labarin da mujallar Spiegel ta wallafa ya saba wa doka”.

Lauyan ya ce an umarce shi da ya nemi diyyar “bata suna” kan wannan ikirarin da mata take wa dan wasan.

Shahararren dan wasan ya koma kungiyar Juventus ne daga Real Madrid a bana a kan fam miliyan 99.2.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *