Najeriya ce hedikwatar talauci a fadin duniya – Jonathan

Goodluck JonathanHakkin mallakar hotoFACEBOOK
Image captionMista Jonathan shi ne shugaban Najeriya tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce kasar ce hedikwatar talauci da fatara a fadin duniya.

Jonathan ya bayyana hakan ne a sakonsa na bikin cika shekara 58 da samun ‘yancin kan kasar a ranar Litinin, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Bayan ya taya ‘yan kasar murnar zagayowar ranar ‘yancin kan ne, tsohon shugaban ya yi tsokaci wanda a cewarsa kasar ta zama “hedikwatar fatara da talauci.”

Sai dai ya ce hakan ba abu ba ne da zai dore saboda amannar da ya yi cewa ‘yan kasar suna da jajircewa.

A karshe ya yi fatan cewa al’amura za su kyautatu da kuma fatan Ubangiji Ya albarci kasar da al’ummarta.

Sai dai kawo yanzu babu wani martani daga fadar shugaban kasar game da ikirarin na tsohon shugaban.

Kuma ba wannan ba ne karon farko da Mista Jonathan ya fara sukar manufofin gwamnatin Shugaba Buhari, wato mutumin da ya gaje shi a shekarar 2015.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *