Satar kudaden Najeriya yanzu ta zama labari – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce satar kudin gwamnati da kwangilolin bogi yanzu sun zama tarihi a kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya gabatar wa ‘yan kasar a ranar cika shekara 58 da samun ‘yancin kan Najeriya daga Turawan mulkin mallaka da aka watsa kai-tsaye a kafofin talabijin na kasar.

Ya ce gwamnatinsa ta samu ci gaba wajen kwato biliyoyin kudaden da aka sace inda yana mai cewa satar kudaden gwamnati da kwangilolin mai na bogi sun zama labari.

Ya ce gwamnatinsa ta yi kokari wajen samar da ayyukan ci gaba da suka shafi gina hanyoyi da layin dogo da gina gadoji da makarantu da inganta lantarki.

Tsaro

Shugaban ya fara jawabin ne da matsalar tsaro musamman rikicin Boko Haram da na makiyaya da manoma.

Ya bayyan irin nasarorin da aka samu a yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashi da kuma kokarin magance rikicin makiyaya da manoma da ya addabi wasu jihohin kasar.

Buhari ya yi alkawalin cewa gwamnatinsa za ta yi kokarin kawo karshen rikicin da kakkabe ‘yan Boko Haram tare da tabbatar da tsaro a yankin.

Ya kuma yi jinjina ga jami’an tsaron kasar ga kokarin da suke na tabbatar da tsaron kasa inda ya ce za a ci gaba da karfafa masu gwiwa da ba su taimakon da ya kamata da iyalansu.

Har ila yau ya ce za su ci gaba da ba da goyon baya ga kungiyoyin sa-kai da hukumomin jiha da na kananan hukumomi da shugabannin addini wajen gano hanyoyin magance rikicin makiyaya da manoma.

Hakazalika ya yi kira ga ‘yan Najeriya na gida da waje da su yi watsi da yadda ake danganta rikicin makiyaya da addini da kuma kabilanci.

Tattalin arziki

Game da batun tattalin arziki, shugaban ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin samar da yanayi mai kyau ga masu saka jari na kasashen waje a Najeriya.

Ya kuma ce sannu a hankali suna bin matakai na farfado da dajarar Naira da rage hauhawan farashin kayayyaki.

Shugaban ya kuma tabo batun inganta harkar noma da hako ma’adinai inda ya ce gwamnatinsa na kokarin gina tattalin arzikin da za a rage dogaro da man fetur.

Zabe

Hakazalika ya tabo batun zabe inda ya ce burinsa shi ne tabbatar da sahihin zabe tare da tabbatar da ‘yancin da doka ta ba hukumar zabe domin gudanar da aikinta.

“Samun ci gaban mulkin dimokradiyya ba abu ba ne mai sauki da za a cimma nan take dole sai an dauki lokaci,” in ji shugaban.

Ya ce wannan shi ne muhimmin darasin da Najeriya ta koya a shekaru 58 na samun ‘yancin kai.

Daga nan ya yi kira ga al’ummar kasar su guji yada maganganun tayar da hankali, su rungumi zaman lafiya da juna da kuma ci gaban Najeriya.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *