Dalilan da ya sa na bar gwamnatin Buhari — Ministar mata

Politics
aisha alhassanHakkin mallakar hotoAISHA ALHASSAN

Ministar harkokin kula da al’amuran mata a Najeriya, Aisha Jummai Alhassan, wacce aka fi sani da Mama Taraba, ta yi murabus.

Ministar ta yi murabus ne bayan da aka gaza tantance ta a cikin masu son tsayawa takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a jihar Taraba wanda za a gudanar da zaben fitar da gwani a cikinsu a ranar 30 ga watan Satumba.

A cikin wata wasika da ta rubutawa shugaban kasa a ranar 29 ga watan Satumbar 2018, Aisha Alhassan, ta ce ba a yi mata adalci ba da aka ki tantanceta a cikin ‘yan takarar tun da dai ai itama ta sayi fom din takarar gwamnan kamar kowa, kuma ta kasance mai biyayya ga jam’iyyar ta APC tun shekarar 2014.

Ta shaida wa shugaban kasa a cikin wasikar cewa, ta yanke shawarar sauka daga mukaminta ne saboda rashin tantance ta da jam’iyyar ta yi a matsayin ‘yar takarar gwamna a jihar Taraba.

Aisha Alhassan ta ce ‘ Idan har ban cancanci na tsayawa jam’iyyar APC takarar gwamna ba, to ina ganin ban cancanci kasancewa minista a gwamnatin APC ba’.

Saukarta daga mukamin nata ya zo ne kwanaki biyu bayan jam’iyyarta ta APC taki tantance ta a matsayin ‘yar takarar mukamin gwamna a zaben fidda gwani da za a yi a ranar 30 ga watan Satumba.

Aisha Alhasan a lokacin da ta ke mukaminta na minista ta fito bayyanar jama’a inda ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar. shi ne ubangidanta a siyasa.

Sai dai bayan da tsohon mataimakin shugaban kasar ya bar jam’iyyar APC zuwa PDP, ministar ba ta bishi ba, inda ta hakikance cewa zata ci gaba da kasancewa a APC.

Yanzu haka dai ministar ta yanki katin zama ‘yar jam’iyyar UDP a ranar Asabar ita da wasu mambobin majalisar dokokin jiharta ta Taraba su bakwai.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *