‘Hukumar agaji ta bai wa mutane lalataccen abinci’ a Ghana

News
ghanaHakkin mallakar hotoGHANA

Hukumar kare afkuwar bala’i ta Ghana, NADMO ta amince cewa mataimakin shugaban kasar Mahamudu Bawumia, ya raba wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a arewacin kasar lalataccen man girki.

Man girkin wanda ya lalace a watan jiya, na cikin kayayyakin agajin da shugaban kasar ya raba.

Jami’an hukumar ta Nadmo sun ce an kebe man ne a wani dakin ajiya kuma kamata ya yi a ce an zubar da shi, amma sai aka yi kuskuren hada shi da kayayyakin agaji a lokacin da aka zuba su a mota.

  • Sabon kayan maye ya bulla a Ghana
  • Ghana ta sallami ministan makamashi daga bakin aiki
  • Ghana: Ma’aikatan lafiya na yajin aiki

A halin yanzu dai jami’an na yankin don karbo lalataccen man.

Sai dai kuma, wasu rahotanni na cewa ciwon ciki ya turnuke wasu mutane bayan sun ci abincin da a ka girka da man.

Mai magana da yawun kungiyar Nadmo, George Ayisi, ya shaida wa BBC cewa har yanzu ba a tabbatar da cewa halin da mutanen su ka fada na da alaka da man ba.

Mambobin jam’iyyar adawa ta kasar Ghana sun yi kira da a yi bincike kan yadda kuskuren ya faru.

Ambaliyar ruwan da aka yi a arewacin kasar Ghana ta kashe mutane fiye da 30, ta kuma raba dubban mutane da gidajensu.

GhanaHakkin mallakar hotoGHANA
Image captionAmbaliyar ruwan da aka yi a arewacin kasar Ghana ta kashe mutane fiye da 30, ta kuma raba dubban mutane da gidajensu
BBC Hausa 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *