Wasika daga Afirka: Mece ce alakar motsin kasa da addini da zaben Najeriya?

Reports
A farkon watan nan ne a ka yi girgizar kasa a babban birnin Najeriya Abuja.
Image captionA farkon watan nan ne a ka yi girgizar kasa a babban birnin Najeriya Abuja.

A jerin sakonnin da muka samu daga Afirka, marubuciya ‘yar asalin Najeriya Adaobi Tricia Nwaubani ta dalilin da ya sa motsin kasa a babban birnin Najeriya ya jawo firgici.

Da safiyar 6 ga watan Satumba ina gidana a Abuja, kwance kan gado, sai kawai naji motsin kasa kuma sai na lura cewa ginin yana dan motsawa gefe da gefe.

Tunanina na farko shi ne masu ikirarin jihadi sun kai hari a wani waje.

Jami'an tsaro a shelkwatar Majalisar Dinkin Duniya a Abuja, Najeriya- August 2011Hakkin mallakar hotoAFP
Image captionA shekarar 2011 motar da ke dauke da bomb ta rusa shingayen tsaro a shelkwatar Majalisar Dinkin Duniya a Abuja.
Presentational white space

Amma da ban ji jiniyar motocin ‘yan sanda da kan yi yawo bayan hare-haren abun fashewa ba, sai hankali na ya kwanta.

Babu mamaki motsin da kasar tayi dalilin fasa duwatsu ne da a kan yi a kusa da unguwar Asokoro, inda nake da zama, da ma wasu unguwannin Abuja, birnin da a ka san shi da yawan manyan duwatsu.

Ranar da kasa tai motsi

A yammacin ranar, kiraye-kirayen waya da na samu daga ‘yan uwa da abokan arziki don jin lafiyata, shi ya tabbatar min da cewa motsin da kasar ta yi a unguwarmu bai kai na sauran unguwanni bai, kamar yankin Gwarimpa, unguwar da ke da rukunin gidaje mafi girma a Afirka ta yamma, da kuma unguwar Mpape inda yawanci masu karamin karfi ne ke zaune a cikinta, inda mazauna su ka gudu su ka bar gidajen su saboda tsananin tsoro.

Jaridu sun rawaito cewa kasar ta fara motsi ne a unguwar Mpape tun da rana kuma ta ci gaba har tsakar dare.

Mazauna unguwannin sun bayyana cewa kayayyakin sayarwar sun fado daga kan kantar shaguna kuma sun ji tsoron kada rufin gidajensu su rufto.

Mutane da yawa sun yi tunanin gidajensu zasu rushe.

Sati biyu kafin afkuwar motsin kasar, rushewar wani kango a unguwar Jabi dake Abuja ya zama babban labari.

Rushewar ginin a wata unguwa ta zamani ya jawo mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai ziyara inda abun ya auku.

Ma'aikatan agaji a inda ginin ya fadi a Abuja, Najeriya- Agusta 2018Hakkin mallakar hotoAFP
Image captionRushewar ginin ya jawo cece-ku ce a watan Agusta

‘Yan kwanaki bayan motsin kasar, wanda aka ji a unguwanni daban-daban a birnin Abuja tsakanin 5 ga watan Satumba da 8 ga watan Satumba, gwamnati ta fitar da wata sanarwa wacce ta tabbatarwa da mazauna birnin cewa kada su daga hankulansu.

Presentational grey line
  • Tasirin motsin kasa a Abuja
  • Motsin kasa ya rusa gidaje a ‘Abuja’
Presentational grey line

“Mu na gudanar da bincike domin gano abun da ya faru a makon da ya wuce” inji Idris Abass, Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na birnin.

Watakila abu ne da ya faru haka nan, amma mu na a so mu tabbatarwa da jama’a cewa Najeriya bata cikin yankunan da girgizar kasa zai iya aukuwa.

'Yan kwana-kwana a inda bam din ya tashi a shelkwatar 'yan sanda a Abuja, Najeriya.Hakkin mallakar hotoAFP
Image captionBam din da ya tashi a shelkwatar ‘yan sanda a shekarar 2011 shi ne harin kunar bakin wake na farko da a ka kai a Najeriya.

An hana fasa duwatsu

Kwana daya bayan da Mr Abass ya yi waccan sanarwa, wata hukumar gwamnati ta fitar da sabon bayani kan motsin kasar.

Hukumar bincike ta sararin samaniya (NASRDA) ta tabbatarwa da mazauna birnin Abuja cewar motsin kasar ba abun tashin hankali ba ne, amma sun tabbatar da cewa girgizar kasar ta auku a garin.

Shugaban hukumar bincike ta sararin samaniya Seidu Mohammad ya ce batai karfi sosai ba kuma bai kai damuwar da mazauna unguwannin zasu ji tsoro su gudu daga gidajen su ba.

Presentational grey line

Adaobi Tricia Nwaubani:

Adaobi Tricia NwaubaniHakkin mallakar hotoADAOBI TRICIA NWAUBANI

Yayin da hukumomin gwamnati suka bada bayanaimabanbanta, yawancin yan Najeriya wadanda suka yizurfi a addini sun yanke hukuncinsu”

Presentational grey line

Ya kara da cewa za a lura da yadda kasar ke motsi don yin hasashen da kuma shirya wa afkuwar irin wannan matsalar nan gaba.

Lokaci kadan bayan afkuwar lamarin, wata hukumar gwamnati ta janyo rade-radi bayan da ta sanar da dage ayyukan fashe-fashen dutse a Abuja.

Amma karamin ministan ma’adanai da karafa Abubakar Bawa ya jaddada cewa ba zai ce “motsin kasar ya auku ne saboda aikin hakar ma’adamnai ba har sai an gama bincike”.

  • An yi girgizar kasa mai karfi a Botswana
  • Girgizar kasa ta kashe mutum 330 a Iran da Iraq
Presentational grey line

Yayin da hukumomin gwamnati suka bayar da bayanai masu karo da juna, yawancin yan Najeriya da su kai zurfi a addini sun yanke hukuncinsu.

Wasu suna ganin cewa alama ce ta cewa Allah na fushi da kasarmu bisa wani dalili.

Wasu na ganin cewa gargadi ne ga Shugaba Muhammadu Buhari, watakila a kan tsarin mulkinsa ko kuma burin sa na kara tsayawa takarar zabe a shekarar 2019 duk da rashin mayar da hankali a aiki a shekara uku da rabin da ya yi mulki.

Wasu kuwa na ganin cewa motsin kasar kira ne ga mutane da su yawaita yin addu’a ga kasar, idan ba haka ba girgizar kasa ta shiga jerin masifun da suka addabi kasar ciki har da: rikicin manoma da makiyaya da yaki da ‘yan boko haram da rikicin kabilanci da kuma durkushewar tattalin arziki.

Abu ne mai wuya mutum ya yi tunanin yadda Najeriya za ta yi idan girgizar kasa ta auku, yayin da take fama da wadannnan bala’o’in da su ka jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *