Manyan ‘Yan Jaridar Nijeriya Sun Yi Hasashen Rugujewar Siyasar Kwankwaso A Jihar Kano

 

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

Biyo Bayan Tsayar Da Surikinsa Abba Kabir Yusuf A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano, Ya Sa Wasu Manyan ‘Yan Jarida Sun Yi Hasashen Hakan Zai Iya Ba Wa Ganduje Damar Maimaita Mulkin Jihar Kano A Karo Na Biyu.

Abdulaziz Abdulaziz

Gogaggen dan jarida da ya ke aiki da jaridar Premium Times, hannunka mai sanda yayi, ta hanyar kawo wasu baituka daga cikin wakar mawaki Marigayi Dakta Mamman Shata, tare da sa hoton Kwankwaso kamar haka:
“Garba kai ka tara abin nan!
Do Allah kar ka bata abinka

Sai ya bata abinsa!
A’a sai ya bata abinsa!

Yadda ya tara abinsa
Sai ya watsa abinsa!”

— Dr Mamman Shata

Ibrahim Sheme

Marubuci kuma babban dan jarida da ya rike manyan mukamai a gidajen jaridu Daban-daban, jigo a kamfanin jaridar Blueprint, ya wallafa a shafinsa na facebook cewa,

“Ina jin cewa, kawo kafi-zurun dan takara kamar Abba Kabir Yusuf, kamar Kwankwaso ya buga kwallo ne a saman raga”

Jaafar Jaafar

Gogaggen dan jarida, wanda ya shahara a yanar sadarwa sakamakon iya suka da barkwanci, a yanzu kuma shugaban kamfanin jaridar Daily Nigerian Hausa da Turanci, shima ya wallafa a shafinsa na facebook cewa:

“Bari na bayyana k’arara cewa, zabin Abba MUTAKABBIR Yusif akwai dambarwa”

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *