‘Yan sanda sun hana lalata fostar ‘yan takara a Akwa Ibom

A lokacin yakin neman zabe ana yawan yaga wa 'yan siyasa fotan kamfe dinsuHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA lokacin yakin neman zabe ana yawan yaga wa ‘yan siyasa fotan kamfe dinsu

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya, Adeyemi Ogunjemilusi, ya nuna takaicinsa game da yadda wasu mutane suke bata fostar ‘yan siyasar da ra’ayinsu bai zo daya ba.

Sanarawar ta kara da cewa: “Daga yanzu duk wanda aka kama yana cirewa ko gogewa ko kuma lalata fostar ‘yan takara ko kuma allon tallar abokan hamayyarsu, ko kuma wadanda aka kama suna karya dokar zabe, za a kama tare da hukunta su bisa dokokin kasa.”

Sanarwar, wadda kakakin rundunar Odiko MacDon ya fitar, ta yi kira ga ‘yan siyasa a jihar ta Akwa Ibom da magoya bayansu su kaurace wa siyasar kiyayya da kalaman batanci ko kuma duk abin da zai janyo matsala a jihar.

  • Najeriya: An haramta zuwa zabe da wayar salula
  • Facebook da Twitter sun sha tsauraran tambayoyi kan zabe

Kwamishinan ya tabbatar wa mutanen jihar cewar rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya yi kokarin tayar da hankali a jihar.

A Najeriya dai a lokacin da zabe yake karatowa ana yawan samun ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan siyasa da abokan hamayyarsu inda wannan ke janyo tashin hankali a wasu lokuta.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *