Birtaniya na shirin hukunta sojin Myanmar

News
Sojin Bama sun daidaita kauyukan jihar Rakhine
Image captionDubban musulmin kabilar Rohingya ne sukai gudun hijira zuwa makofciyarsu Bangladesh a bara, dan gudun kisan kare dangin da sojin Myanmar ke musu

BBC ta gano Birtaniya na shirin kafa kotun ta musamman dan gurfanar da sojojin Myanmar.

Rahoton majalisar dinkin duniya ya jera nau’o’in cin zarafin da aka yi wa yara ‘yan Rohingya, da Fyade, da kisa, da lalata daukacin kauyukan da suke rakabe a jihar Rakhine.

Ana sa ran sakataren harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt wanda bai jima da kai ziyara Myanmar ba, zai bukaci hadin kan kasashen duniya kan wannan shiri a gaban zauren majalisar dinkin duniya a mako mai zuwa.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *