Kwantainoni cike da dala miliyan 60 sun yi batan-dabo

News
Ex-football star George Weah was elected president of Liberia in DecemberHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA watan Disambar bara ne aka zabi tsohon tauraron kwallon kafa George Weah a matsayin shugaban Laberiya

Gwamnatin Laberiya ta ce tana bincike game da abin da ya faru da manyan kwantainoni biyu cike da kudaden da aka buga a kasar waje kuma aka shigar da su kasar tsakanin watan Nuwamba da na Agustan bana.

An ce kudaden, wadanda suka kasance takardar kudaden kasar da suka kai dala miliyan 60, sun bace.

Wani rahoto ya ce kwantainonin da suke makare da kudade sun bar tashar jirgin ruwan kasar a babban birnin kasar, Monrovia, a karkashin sa idon jami’an tsaro a watan Maris, kuma an zaci sun nufi babban bankin kasar ne, amma sun bace.

Hakazalika an kasa ganin kudaden da aka kawo ta babban filin saukar jirage na kasa-da-kasa.

  • Bincike: Masu cutar Ebola na samin tabin hankali
  • Habibu Sani Babura: Malamin da bai san nakasa ba

Ma’aikatar shari’ar kasar ta nemi mutane su kwantar da hankalinsu yayin da wani kwamitin jami’an tsaro ke gudanar da bincike kan lamarin.

Ministan watsa labarai, Eugene Nagbe, ya shaida wa gidan rediyon kasar cewar Shugaba George Weah, wanda aka rantsar a watan Janairu, bai ji dadin rashin sanar da shi matsalar a kan lokaci ba.

“Abin tashin hankali ne,” in ji Mista Nagbe.

Kawo yanzu dai ba a kama kowa ba game da lamarin, amma ministan watsa labaran kasar ya ce yana da yakinin cewar za a gane hakikanin abin da ya faru a lamarin.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.