An yi garkuwa da gawa don neman kudin fansa

'Yan sandaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

‘Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da garkuwa da gawar wata tsohuwa a kudu maso-gabashin Najeriya.

‘Yan sanda daga Oweri, babban birnin jihar Imo, sun ce mutanen sun sace gawar ne daga wajen ajiye gawa a wani asibiti, kuma suka kai ta daji suna masu neman naira miliyan hudu a matsayin kudin fansa daga asibiti da kuma iyalan marigayiyar, in ji ‘yan sanda.

An kama wadanda ake zargin, wadanda a baya aka taba samu da laifi, a wani samamen da aka kai musu.

Tuni dai akai mayar da gawar ga iyalan marigayiyar.

  • An yi garkuwa da mutane da dama a Zamfara
  • Yadda muka kashe ‘mai garkuwa da mutane’ a Fatakwal— Sojoji

Kwanan nan aka sako mutanen daga gidan yari bayan sun yi zaman kaso bisa laifin garkuwa da mutane.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *