Kun san wanda Buhari ya nada shugaban hukumar DSS?

Yusuf Magaji BichiHakkin mallakar hotoCREDIT: STATE HOUSE
Image captionFadar shugaban Najeriya ta ce Yusuf Magaji Bichi kwararren ma’aikacin leken asiri ne

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon shugaban hukumar tsaro ta cikin gida (DSS).

Nadin ya fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Satumba 2018.

Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce sabon shugaban kwararren jami’in leken asiri ne.

Yusuf Bichi ya taba zama daraktan hukumar ta DSS a jihohin Jigawa da Naija da Sokoto da Abia.

  • Da gaske ne EFCC ta samu kudi a gidan Lawal Daura?
  • Osinbajo ya kori shugaban DSS Lawal Daura

Sanarwar da Garba Shehu ya fitar ta ce jami’in ya sami horo a bangarorin leken asiri da bincike da bayar da kariya da kuma tattara bayanai.

Ya yi kwasa-kwasai a Birtaniya da kuma Najeriya, sannan ya rike mukamai da dama a hukumar ta ‘yan sandan ciki ta kasar.

Muhammadu BuhariHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionSabon shugaban da Buhari ya nada zai maye gurbin mukaddashin shugaban hukumar da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbaji ya nada.

Sabon shugaban na hukumar ta DSS ya fara aikin tsaro a ofishin gwamnatin Kano, daga nan kuma sai ya shiga hukumar ‘yan sandan ciki ta Najeriya (NSO), sannan ya zama mai shigar da kara a hukumar DSS.

Ya yi makarantar sakandaren Dambatta a Kano, sannan ya halarci kwalejin share fagen shiga jami’a ta Kano, ya kuma karanci kimiyyar siyasa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *