Amina: ‘Bashi ya yi wa kasashen Afirka katutu’

Amina Muhammad
Image captionAmina Muhammad ta nuna damuwa kan basussukan da kasashen nahiyar Afirka ke karba daga kasashen waje

Ana ci gaba da nuna damuwa kan kalaman mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina Muhammed ta furta kan basussukan da kasashen nahiyar Afirka ke karbowa ciki har da Nigeria, inda ta nuna fargaba game da basussuka da kasar ke ci a baya-bayan nan da kuma wasu kasashen nahiyar Afirka.

Inda ta bukaci hukumar bayar da lamunin ta duniya ta duba bukatun kasashe masu tasowa kan rajin na samun ci gaba, amma a bisa tafarkin da ya dace.

Ta kara da cewa, ”wasu daga cikin damuwar da muka nuna a taron da aka yi a kasar China a kwanakin baya, shi ne maganar bashin nan ta na da girma musamman idan mu ka yi la’akkari da gwagwarmayar shekaru da tsohuwar ministar kudin Nigeria Dr Ngozi Ikwenje Iweala ta yi dan ganin an samu saukin bashin”.

  • Buhari ya ce hakura da yaki da rashawa cin amanar ‘yan Najeriya ne
  • Buhari ya nada sabon shugaban hukumar DSS

Sai dai sanata Shehu Sani, shugaban kwamitin majalisar dattijan Najeriya kan bashin da ake bin kasar, ya shaida wa BBC cewa gwamnatocin baya da suka ciwo bashin makudan kudade babu wani tartibin abu guda da za a nuna a san da kudin da aka ciwo bashi aka yi wa ‘yan kasa.

Ya ce lokacin da gwamnatin APC ta karbi mulki daga hannun PDP a shekarar 2015, ana bin Najeriya bashin dala biliyan goma sha daya ne. A halin da ake ciki kuma ya kai dala biliyan ashirin da biyu hakan na nufin ya rubanya.

”Amma bashin da aka ciwo karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari, an tafiyar da su ne bisa ayyukan cigaban kasa da ababen more rayuwa da ake gani a zahiri. Yawancin ayyukan da aka yi a zahiri ana gani a kasa, gwamnati ko ‘yan kwangila ko ‘yan siyasa ba su yi ruf da ciki akan kudaden ba,” in ji Shehu Sani.

Fargabar da ake nunawa dai ita ce ta yaya Najeriya za ta biya bashin makudan kudaden, idan aka yi la’akkari da yadda tattalin arzikin duniya ke hawa da sauka.

Wasu ‘yan kasar dai sun nuna rashin jin dadi kan wannan bashi, inda wasu ke tababar ko ta yaya Najeriya za ta iya biyan biliyoyin dalolin da ake bin ta bashi.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *