SANATA WAMAKKO YA TALLAFAWA WANI MAI KARAMIN KARFI

News

 

Daga Jamilu Sani Rarah Sokoto

Tsohon Gwamnan Sokoto kuma Sanatan Sokoto ta Tsakiya Aliyu Magatakarda Wamakko ya tallafawa wani mai sana’ar sayar da kwakwa da zunzurutun kudi har naira dubu hamshin domin ya kara jari.

A jiya ne bayan kammala sallar idi a mahaifar Sanatan dake karamar hukumar Wamakko, inda Sanatan ya yanka ragonsa na layya bayan kammalawa kuma sai ya zauna domin kallon yadda ake aikin raguna. Sai wannan mai sayar da kwakwar ya zo wucewa, inda Sanata Wamakko ya kira shi ya tambaye shi nawa ne kudin kwakwar gaba daya?

Bayan mai sayar da kwakwar ya bayyana adadin kudinta dubu hudu kawai sai Sanatan ya ba shi wannan makudan kudade. Abinda ya sanya wannan Bawan Allah zubar da hawaye.

@Rariya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *