Barawon Ragon Layya Ya Shiga Hannu A Garin Yola

 

Dubun wani ɓarawon rago ya cika a kasuwar dabbobi dake garin Yola babban birnin jihar Adamawa. Inda ya zo sayar da ragon da ya sata amma sai ya haɗu da rashin sa’a. Inda ya shiga hannun wanda ya yi wa satar, wato mai ragon tare da ‘ya’yanta sun riga shi zuwa kasuwar don ganin wanene zai zo da ragon nasu sayarwa bayan da suka wayi gari basu ga ragon ba.

Allah ya taimakesu suka ci karo da ɓarawon ragon yayin da yake kokarin shigowa da ragon kasuwar.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *