Mawakiya Aretha Franklin ta rasu tana da shekara 76

Aretha Franklin performing in LA in 2012Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Shahararriyar mawakiyar nan ‘yar Amurka Aretha Franklin, ta rasu a birnin Detroit, tana da shekara 76.

Franklin tana da wakokin kimanin 20 da suka fi fice a Amurka a tsawon shekara 70 da ta yi tana wake-wake.

A watan Nuwambar bara ne ta yi wasan karshen a birnin New York.

A wata sanarwa da iyalanta suka fitar ta ce: “A wannan yanayi da yau muka samu kanmu, mun rasa kalaman da za mu yi amfani da su wajen bayyana wannan al’amari.”

“Mun rasa wata babbar ginshiki ta wannan gida. Marigayiyar tana matukar kaunar ‘yaya da jikoki da sauran mutanen gidan nan.”

Har ila yau an bayyana cewa Kansar matsarmama ce ta yi ajalinta.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *