An yi tir da tsare dan jaridar Premium Times a Najeriya

News
Samuel OgundipeHakkin mallakar hotoPREMIU TIMES
Image captionAn kama Samuel Ogundipe ne bayan ya kwaramta wata wasikar da sufeto janar din ‘yan sanda ya rubuta.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da hakkin ‘yan jaridu a Najeriya na ci gaba da Alla-wadai tare da kira a gaggauta sakin dan jaridar nan na Premium Times Samuel Ogundipe, da jami’an tsaro ke tsare da shi.

A cikin labarin nasa wanda wasu kafafan watsa labarai suka dauka, dan jaridar ya fallasa wata wasika da hukumar ‘yan sanda ta aike wa Mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo.

Wasikar mai dauke da shafi biyar, ta bayyana yadda tsohon shugaban hukumar DSS Lawal Musa Daura ya umarci jami’ansa su datse majalisar ba tare da neman izinin fadar gwamnati ba.

To sai dai a wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ranar Alhamis ta ce an kam Samuel ne bisa zargin sata, da mallakar bayanai ta haramtacciyar hanya, abinda zai iya barazana ga tsaron kasa, sannan da haifar da tasin hankali a kasar.

Sanarwar da kakakin rundunar DCP Jimoh Moshood ya sanyawa hannu ta ce tuni aka gurfanar da dan jaridar a gaban kotu, bisa tuhumar saba dokar kiyaye sirrin gwamnati, da laifukan da suka shafi kafofin internet.

  • Akwai ‘maciya amana’ a cikin ma’aikatan EFCC —Magu
  • ‘Buhari ba ya fuskantar matsin lamba kan takararsa’

To sai dai tuni kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi tir da abin da ta kira tauye ‘yanci albarkancin baki da matsi ga ‘yancin aikin jarida a Najeriya.

A ranar Laraba ma Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa, NUJ da kungiyoyin fararen hula da kuma daidaikun mutane sun nemi a saki dan jaridar ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba.

A ranar Alhamis ma ‘yan jarida sun gudanar da zanga-zangar neman sako dan jaridan a hedikwatar ‘yan sandan Najeriya.

Wani edita a kamfanin na Premium Times Muhammad Lere ya shaidawa BBC cewa kafin a cafke dan jaridar, sai da’yan sanda suka soma tsare wata ma’aikaciyarsu mai suna Azeezat Adedigba da Babban Editan Jaridar Musikilu Mojeed, amma daga baya aka sake su.

‘Yan sandan dai sun bukaci ala tilas Mista Ogundipe ya bayyana inda ya samo labarinsa, wanda yin haka ya saba wa ka’idar aikin jarida, in ji Muhammad Lere.

Wannan layi ne

Wasikar da ake zargin Samuel da kwarmatawa dai, ta kunshi tsame hannun ‘yan sanda kan hana wasu sanatoci shiga majalisar tarayya da ke Abuja.

Wasikar mai shafi biyar ta ambato Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar yana yiwa mukaddashin shugaban kasar karin bayani kan tsare tsohon shugaban DSS Lawal Daura, da binciken da ake gudanarwa a kansa.

Takardar ta kuma bayanan irin matakan da ake dauka na bincikar wasu jami’an hukumar da suna yi aikin tare majalisar, da binciken na’urori da kamfutocin da jami’an hukumar DSS ke amfani da su wajen musayar bayanai.

Hakazalika Sufeto Janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris ya nesanta kansa da abin da ya faru tare da bayyana cewa Lawal Daura ya yi gaban kasan ne a bisa son zuciya irin ta siyasa.

Haka kuma takardar ta ambaci wasu shawarwari da rundnar ‘yan sandan ke baiwa gwamnati kan batun hana wasu sanatoci shiga majalisar.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.