Amarya ta ‘kashe’ jaririn kishiyarta da tafasasshiyar miyar kubewa

jigawa policeHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionRundunar ‘yan sandan Najeriya

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa a arewacin Najeriya ta ce tana tsare da wata amarya wadda ta watsa wa uwargidanta tare da danta dan wata 10 tafasasshiyar miyar kubewa a jikinsu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, CP Abdu Jinjiri ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Gantsa da ke karamar hukumar Buji ta jihar.

Sai dai ya ce jajririn ya mutu sanadiyyar abin da ya faru.

CP Jinjiri, ya ce akwai rashin jituwa a tsakanin kishiyoyin.

Amaryar wadda ba ta wuce shekara 20 da haihuwa ba tana dakin girki ne a lokacin da uwargidan, rungume da danta, ta shiga dakin dafa abincin, daga nan, sai amaryar ta fara mayar mata da magana.

  • Mata biyar da suka fi fice a duniya
  • Dole Bukola Saraki ya bar majalisa —Akpabio

Daga nan sai cacar baki ta kaure. Ba tare da ba ta lokaci ba ne kuma amaryar ta dauki tukunyar miya tana tafarfasa ta watsa wa uwargidan da danta a jikinsu.

Bayan ta watsa musu miyar ne amaryar kuma ta fara ihu tana neman a kawo musu dauki.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce uwargidan tana babban asibItin Dutse tana karbar magani, kuma duk jikinta ya daye, amma yaron ya rasu.

Kwamshinan ‘yan sandan jihar CP Bala ya bayar da umarnin a kai amaryar da ta aikata lamarin sashen binciken kwakwaf domin gudanar da bincike da kuma yi mata hukuncin da ya dace.

BBC ta yi kokokarin jin ta bakin mijin matan wato Malam Hamza, amma wayarsa a rufe.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *