Da gaske ne EFCC ta samu kudi a gidan Lawal Daura?

Kudin da EFCC ta gano a Lagos a 2017Hakkin mallakar hotoFACEBOOK/ EFCC
Image captionBankado kudaden da EFCC ta yi a Lago a watan Afrilu na 2017 ya ja hankalin ‘yan Najeriya a lokacin.

Ranar 7 ga watan Agusta ne dai mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya kori Lawal Daura daga mukamin shugaban rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) bayan jami’an hukumar sun hana sanatocin Najeriya shiga majalisa.

Mukaddashin shugaban kasar ya yi tir da aikin da ya bayyana cewa ya ci karo da tsarin mulkin Najeriya tare da shan alwashin ganowa da hukunta wadanda ke da hannu a aikin.

Da yammacin ranar ne dai Osinbajo ya gana da sabon shugaban hukumar da ya maye Daura, Matthew B. Seiyefa, da kuma shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon gasa, Ibrahim Magu.

Washe gari dai rahotanni sun ce jami’an hukumar EFCC sun kai samame gidan tsohon shugaban hukumar DSS, Ita Ekpeyong.

Bayan nan kuma aka fara yada wani bidiyo a shafukan sada zumunta wanda ake ikirarin cewar bidiyon kudin da aka samu a gidajen Tsohon shugaban DSS, Lawal Daura ne.

  • Ra’ayi Riga: Shin matakin korar Lawal Daura ya dace?
  • Hukumar EFCC za ta ‘binciki’ Lawal Daura
  • Da sanin Buhari aka kori Lawal Daura – Fadar shugaban Najeriya

An yi ta yayata wani labari ma wanda yake ikirarin cewar an samu tsabar kudi naira biliyan 21 da da bindigogi 400 da kuma dubban katunan zabe na din-din-din a gidan Lawal Daura na Katsina.

Sai dai kuma binciken BBC ya gano cewar wannan bidiyon na kudaden da EFCC ta gano ne a wani gida daga cikin jerin gidaje masu alfarma da ake kira Osborne Towers a unguwar Ikoyi ta Legas.

Hukumar EFCC ta fitar da hotuna da bidiyo na aikin a wancan lokacinHakkin mallakar hotoFACEBOOK/EFCC
Image captionHukumar EFCC ta fitar da hotuna da bidiyo na aikin a wancan lokacin

Kuma a cikin watan Afrilun shekarar 2017 ne EFCC ta yi aikin wanda a yanzu ake ci gaba da yada bidiyon.

Bayan haka kuma hukumar DSS ta fitar da wata sanarwa inda ta ce bidiyon ba na gidan stohon shugabanta bane.

Hakzalika, sanarwar da kakkin hukumar DSS, Tony Opuiyo, ya fitar, ta ce ba gaskiya ba ne cewar an sami tsabar kudi Naira biliyan 21 da bindigogi 400 da kuma dubban katunan zabe na din-din-din a gidan Daura.

Yayata labaran karya dai na dada zama ruwan dare a kasashen duniya, musamman a lokutan zabe.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *