LABARAI A TAKAICE

News

 

*Hajjin Bana: Zuwa safiyar Larabar nan, an kwashi maniyyata daga Nalijeriya, zuwa kasar Saudiyya, adadin mutum dubu 19,091. yawan jiragen da suka yi jigila na kamfanonin Maxair, Flynass da Medview sunyi sawu 46. Madogara: NAHCON*

*Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kwabe shugaban hukumar tsaron farin kaya DSS Lawal Daura daga mukamin sa da bukatar nan take ya mika ragama ga mabiyin sa a mukami a rundunar.*

*Sanarwar dai ta fito ne daidai lokacin da jami’an tsaro su ka kange mashigar majalisar dokokin Najeriya da zargin barin wasu su shige cikin yunkurin tsige shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.*

*Tun farko dai shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki ya ba da umurnin a zo a taron shugabannin majalisar don duba yadda za a bullowa bukatar sashen zartarwa na bude majalisar don duba wani karamin kasafin kudi da ya shafi hukumar zabe.*

*Zuwa yanzu dai za a ce yunkurin tsige Saraki bai samu nasara ba kuma majalisar na ci gaba da kasancewa a rufe har watakil ranar dawowa 25 ga watan gobe.*

*Mafi girman darakta a hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS Mathew Sieyefa ya zama mukaddashin shugaban hukumar biyo bayan kwabe babban daraktarn hukumar Lawal Daura.*

*Jami’in labarun ofishin mukaddashin shugaban Najeriya Laolu Akande ya baiyana haka da nuna Sieyefa zai rike wannan mukami har daukar mataki na gaba. Sieyefa dai wanda dan asalin jihar Bayelsa ne a kudu maso kudancin Najeriya, shine mataimakin babban daraktan hukumar a sashen aiyuka.*

*Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta nesanta kan ta daga hannu a aikin jami’an da su ka hana ‘yan majalisar dokokin Najeriya shiga majalisar da barin wasu su shiga. Rundunar ta bukaci mutane su yi watsi da rahoton da ke cewa ‘yan sanda na cikin wadanda su ka dauki wannan mataki kuma rundunar na mutunta doka da oda da kare sassan gwamnati su yi aikin su.*

*Jami’in labarun rundunar Moshood Jimoh bai kammala da cewa za a gudanar da bincike don kamo wadanda su ka toshe kofar shiga majalisar ba.*

*Tuni rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanya jami’an ta su ka damke tsohon babban daraktan hukumar DSS Lawal Daura jim kadan bayan kwabe shi daga mukamin sa. Yanzu dai Lawal Daura na hannun ‘yan sandan duk da ba su ba da sanarwar gudanar da wani bincike ko tunanin zuwa kotu ba.*

*Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci kasashe su daina duk wata huldar arziki da kasar Iran bayan abun da ya kira takunkumi mai tsanani da Amurka ta sanyawa Iran din. Takunkumin dai ya biyo bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar sassauci kera makamin kare dangi da Iran din ke yi. Trump ya ce duk kasar da ke hulda da Iran ba za ta yi hulda da Amurka ba.*

*Ibrahim Baba Suleiman*
*Jibwis Social Media*
*25-Dhul-Qa’adah-1439*
*08-August-2018*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *