APC Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yiwa Sanata Shehu Sani

Jam’iyyar APC ta bayar da sanarwar janye matakin da ta dauka na dakatar da dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani.

Kakakin jam’iyyar na Kasa, Yekini Nabena ya ce, matakin na daga cikin kokarin maido da zaman lafiya a reshen jam’iyyar na jihar Kaduna ne inda ya umarci shugabannin APC na mazabar dan majalisar kan su bi wannan umarnin.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *