‘YAN KWANKWASIYYA SUN MIKA WUYA GA APC A JIHAR JIGAWA

 

Mabiya Darikar Kwankwaasiyya Suna ci Gaba Da Yi wa Tafiyar Kwankwaasiyya Tawaye Tun Ranar Da Shugaban Kwankwaasiyya Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, Ya Bayyana Ficewa Daga Jam’iyyar APC Zuwa PDP.

Jiya Juma’a Wasu ‘Yan Mabiya Darikar Kwankwaasiyya Suma Sun Ajiye Jajayen Hulunansu, Inda Kwamishinan Kudi Na Jihar Jigawa Hon Namadi Kafin Hausa, Ya Jagoranci Karbarsu.

Mabiyan Na Kwankwaasiyya Sun Bayyana Cewar Tsohon Jagoran nasu Ya basu Kunya, Da Har Ya Fifita Kanshi Fiye Da Al’umma.

Da yake jawabi Kwamishinan Kudi Hon Namadi Yace Sun yi Farin Ciki Sosai Bisa Yadda Allah Ya Ganar Da Mabiyan Kwankwasiyya Gaskiyay Kuma Suka yi Aiki Da Gaskiya, Domin A Cewar shi Duk Mai Kishin kasa Ba zai Ki Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

An Karbe su ne A Maimuna Millennium Dake Karamar Hukumar Hadejia.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *