Ina Matukar Jinjina Ga Al’ummar Jihar Bauchi Da Gwamna M. A Abubakar, Inji Shugaba Buhari

 

…bayanai masu sosa zuciya daga bakin Buhari

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa al’ummar jihar Bauchi da Gwamnansu Barista Mohammed Abdullahi Abubakar, bisa tarbar da suka yi masa.

Shugaba Buhari yace “jihar Bauchi gari ne wanda nake matukar alfahari da shi a tarihin siyasata. Ina da dumbin masoya wadanda suke matukar kaunata da ban san iya adadin su ba. Na yi imanin suna son ganina amma hakan ba ta samu ga wasu ba, ina matukar gode maku kuma ina matukar alfahari da ku”.

“Sanin kowa ne cewa a jihar Bauchi aka fara kirkirar ‘a kasa a tsare’. A wannan lokacin wasu sun rasa ransu. Wasu sun samu nakasa a jikin su. Amma duk da haka ba su gaza ba wajen nuna kauna a gareni. Ina kaunar ku, ina alfahri da ku, ina kuma godewa Gwamnan ku domin ina matukar alfahari da M. A Abubakar. Mutum ne mai gaskiya da rikon amana. Idan har kuna kaunata to na umarce ku da ku kaunaci M. A Abubakar” Inji Shugaba Buhari.

Shugaba Buhari ya kara da cewa “ba ni da burin na cuci kowa a mulkina. Ina tsoron abinda Allah zai tambaye ni ranar gobe kiyama, na rike mukamai kala – kala a Nijeriya amma har yanzu gida biyu kadai na mallaka a kasar nan. Shekaru na 75, ta Allah za ta iya kasancewa a gare ni a koda yaushe. A don haka babban burina shine in gina kasata, ta yadda koda bayan bana raye za a yi alfahri da abinda na bari, kuma jikokin mu su yi alfahri da mu”.

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa “Mulki na Allah ne, kuma shine yake bayar da shi ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so. Shi ya bani mulki kuma, zai iya karbe shi a koda yaushe koma ya dauke ni baki daya. A don haka ina kira ga dukkan magoya bayana na jihar Bauchi da ma duk fadin Nijeriya, da cewa kada ku zagi kowa amma ku yada abin ci gaba da muka kawo a kasar nan”.

A karshe shugaba Buhari ya yi kira ga al’ummar Bauchi ta kudu, da cewa idan har suna kaunar shi, to su zabi wanda jam’iyyar APC ta tsayar, wato Lawal Yahaya Gumau wanda hakan shine zai karawa jam’iyyar karfi a majalisar dattawa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an ga fuskokin mutane da yawa suna zubar da hawaye a lokacin da shugaban yake bayani, ciki har da Gwamnan jihar Bauchi Barista Mohammed Abdullahi Abubakar da Gwamnan jihar Kano Dakta Umar Abdullahi Ganduje.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *