APC Ta Rusa Shugabanninta Na Kwara Bisa Biyayya Ga Saraki

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na Kasa ya rusa shugabannin jam’iyyar reshen jihar Kwara bisa biyayya da suke yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki wanda ake ganin ya rigaya ya yanke shawarar komawa PDP daga jam’iyyar ta APC.
Kwamitin gudanarwa na APC ya nada Hon. Bashir Bolarinwa a matsayin Shugaban riko na jam’iyyar. Tun da farko dai, Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed wanda dan asalin jihar Kwara ne, ya koka kan cewa shugabannin APC na jihar suna yiwa PDP aiki ne.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *