“Buhari Ikon Allah Ne” – In ji Gwamna Ganduje

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ikon Allah ne, wanda kuma Allah Ya ke kare shi daga magabta wadanda ba sa fatan cigaban kasa da gina al’umma.
Ya ce Allah ne Yake kare shugaban kasar daga kulle-kullen masu shirya masa makarkashiya, “…kuma wani abin sha’awa da karfafa gwuiwa shine, kullum ta duniya, kishin cigaban kasar nan ne a gabansa,” ya tabbatar da hakan.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake karbar bakuncin ‘yan kungiyar kwallon kafar nan ta Bandirawo Babes a fadar gwamnatin jiha, wadanda su ka je su nuna masa kofin da suka ci bayan kammala gasar kwallon kafar da su ka yi.
Haka nan kuma sun je saboda su ba gwamnan na Kano wata kyauta ta musamman saboda girmama shi da kuma yabawa da ayyukansa na cigaban matasa da yake yi a jihar.
“Ku ne shugabannin gobe, kuma kullum burin shugaban kasarmu mai sanin ya kamata shine a kyautata rayuwarku. Hakan kuma shine buri da manufofin wannan jam’iyya ta mu ta APC” in ji Gandujen.
Ya kara da cewa, a matsayinsu na masu son kyautatawa al’umma, sun dauki tallafawa matasa da shirye-shiryen dogaro da kai, da kuma ba su ayyukan yi da matukar muhimmancin gaske.
“Da ganinku dai dukkanku kun isa jefa kuri’a idan lokacin zaben 2019 ya zo. Saboda haka ina fatan wadanda ma ba su karbi katinsu na yin zabe ba, da su gaggauta yin hakan kafin lokacin karbar ya kure,” ya ce.
Gwamnan ya kalubalanci abokan adawar jam’iyyar APC wadanda suka fice daga cikin jam’iyyar kwanan nan, da cewa, wannan ko a jikinsa (Shugaba Buhari).
Ya tabbatar da cewa abinda magabtan shugaban ke yaki da shi bai wuce dalilin yadda ya dauko hanyar gyara kasa ba. Alhali kuwa su irin wadancan mutane ba gyaran kasa da al’umma ne a ran su ba.
“Mun san cewa yadda kyakkyawar dabi’a da kuma farar zuciya da wannan shugaban namu yake da su, ya kasance a kullum masu kishin kasa sai kara nuna goyon bayansu suke yi gare shi,” in ji shi.
Gandujen ya kammala da cewar, “Ya kamata ranar zabe ku fito kwanku da kwarkwatarku saboda ku zabi shugaba Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC a dukkan matakai. Hakan zai kara ba da damar cigaba da ayyukan da a ka daukowa jama’a saboda cigaban al’umma.”
Daga karshe kuma gwamnan ya yabawa shugabar kungiyar kwallon kafar ta Badirawo Babes, wato Salamatu Galadima, ya yaba da irin wannan kokari da ta yi har kungiyar ta samu nasarar cin gasar kwallon.
Anwar shine Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *