ZABEN 2019: Wani Jakada A Gwamnatin Buhari Ya Ajiye Matsayinsa Domin Komawa PDP

Jakadan Nijeriya a kasar Afrika ta Kudu, Ambasada Ahmed Musa Ibeto ya ajiye mukaminsa, hakazalika yana shirye-shiryen barin jama’iyar APC zuwa PDP da zummar yin takarar kujerar gwamnan Jihar Neja a 2019.
Ahmad Musa Ibeto dai tsohon maitaimakin gwamnan Jihar Neja Mu’azu Babangida Aliyu ne a jama’iyar PDP na tsawon shekaru takwas, inda a karshen wa’adin mulkin su na biyu Ibeto ya fice daga jama’iyar PDP zuwa APC sakamakon rasa damar yin takarar kujerar gwamnan Jihar da yaso ya gaji tsohon ubangidan nasa da sauran matsalolin da sukata faruwa da a tsakaninsa da Babangida Aliyu.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *