An tsige Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kano

majalisar kano

‘Yan majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun tsige Shugaban Majalisar jihar Alhaji Yusuf Abdullahi Ata, bayan da aka shafe tsawon lokaci suna kokarin yin hakan.

A ranar Litinin da safe ne ‘yan majalisar 27 daga cikin 40 suka sanya hannu a kan kudurin tsige Honorabul Ata, ciki har da shugaban marasa rinjaye daya tilo da ke majalisar.

A watan Mayun da ya gabata dai jami’an ‘yan sanda sun yi wa majalisar kawanya, don hana ‘yan majalisar shiga a kokarinsu na tsige shugaban.

‘Yan majalisar dai na zargin kakakin nasu da rashin iya gudanar da aiki, da raba kawunan ‘yan majalisar da kuma zubar da kimar majalisar a idon al’umma.

Sai dai ya musanta aikata wani laifi tun a lokacin.

A yanzu dai ‘yan majalisar sun nada tsohon kakakin Kabiru Alhassan Rurum, wanda ya yi murabus a watan Yulin bara, bisa zargin sa da aikata wasu laifuka da suka shafi cin hanci.

Honorabul Rurum dai shi ne mataimakin Honorobul Ata kafin a sauke shi.

  • Ni da Kwankwaso ne iyayen PDP a Kano – Shekarau
  • Yadda rijiyoyi ke cinye rayukan jama’a a Kano
  • Tsoron Buhari ya sa ake fita daga APC – El-Rufa’i
RurumHakkin mallakar hotoRURUM FACEBOOK
Image captionAn sake nada Alhassan Rurum shugaban majalisa wanda ya yi murabus a bara.
BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *