Ni da Kwankwaso ne iyayen PDP a Kano – Shekarau

Kwankwaso da ShekarauHakkin mallakar hoto@KWANKWASORM

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekaru ya ce ya yi murna da maraba da komawar takwaransa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso jam’iyyar PDP.

A ranar Asabar ne tsofaffin gwamnonin biyu na Kano suka gana wadanda a baya suke hamayya da juna.

Ana sa ran sun gana ne domin tattaunawa game da hadin kansu da kuma ci gaban jam’iyyar PDP.

Wani shafin Twitter mai dauke da sunan Sanata Kwankwaso ya wallafa hoton tsoffin gwamnonin na Kano guda biyu tare da cewa suna gina yadda za su ciyar da Najeriya gaba.

Gabanin ganawar, Malam Ibrahim Shekaru ya shaidawa BBC cewa sun dade suna fatan Allah ya dawo da Kwankwaso domin tun farko ya san karshen alewa kasa.

“Duk wani dan siyasa yana son kari ko da mutum daya ne, kuma mu wannan tagomashi ne gare mu.”

“Ana cin zabe da kuri’a daya ana faduwa da kuri’a daya. mutanen da Kwankwanso ya zo da su karuwa ce ga PDP duk da cewa ba duka za su bi shi ba.” in ji Shekarau.

Ya kuma jaddada cewa ba shigowar Kwankwaso a APC ba ce ta fitar da shi daga jam’iyyar.

Shekarau ya ce batun wanene jagoran PDP a yanzu bai taso ba bayan an tambaye shi ko zai iya bin kwankwaso a matsayin jagoran jam’iyyar a Kano.

“Ba wani ne yake nadi ba na jagora, idan tsarin jam’iyya za a bi, yanzu batun wanene jagora duk bai taso ba.”

“Kwankwaso yana sahun gaba cikin manyan iyayen jam’iyya, idan mun fahimci juna da shi mun zama iyayen jam’iyya muna tare, kuma kafadarmu daya.”

Shekarau kuma ya yi watsi da rade-raden cewa zai koma APC inda yace jita-jita ce kawai. “Ban taba zancen komawa APC da wani ba.”

“Babu wani jami’i na jam’iyyar APC da ya zo min da maganar tayi ko da wasa cewa wai in dawo APC,” in ji shi.

Wasu na ganin hadewar tsoffin gwamnonin na Kano a jam’iyyar adawa, babbar barazana ce ga makomar gwamnantin APC ta Abdullahi Ganduje a Kano.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *