Komawar Kwankwaso PDP Ba Alheri Ba Ne Ga Su Shekarau — Ilyasu Kwankwaso

News

Kwamishinan Raya Yankunan Karkara na jihar Kano, Ilyasu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa komawar Tsohon Gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso PDP ba alheri ba ne ga jam’iyyar saboda zai yi kokarin kwace ikon jam’iyyar ce daga jigogin ta wanda ya hada da Nalam Ibrahim Shekarau.

Kwamishinan ya kara da cewa, Kwankwaso zai tabbatar da ganin ya dasa mutanensa a matsayin ‘yan takarar PDP wanda zai hada har da na kujerar Gwamnan jihar, lamarin da ya ce, zai janyo mafi yawan ‘yan jam’iyyar su canja sheka.

@Rariya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *