Saraki ya gaji sarautar mahaifinsa ta Wazirin Ilori

An nada saraki sarautar Wazirin IloriHakkin mallakar hotoW. ONEMOLA
Image captionDaga Turaki yanzu Saraki ya zama Wazirin Ilori

Sarkin Ilori Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya ba shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki sarautar Waziri.

An yi nadin sarautar ne a wani taro na musamman da masarautar Ilori ta shirya domin Saraki kan nasarar shari’arsa da kotun koli ta wanke shi daga tuhume-tuhume na zargin yin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka lokacin da yana gwamnan Kwara.

Saraki wanda kuma shi ne Turakin Ilori, yanzu ya gaji sarautar mahaifinsa ta Waziri, sarautar da Dakta Olusola Saraki ya rike har zuwa rasuwarsa a 2012.

A farkon watan Yuli ne kotun kolin Najeriya ta wanke Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa, shari’ar da gwamnatin tarayya ta shigar.

Tun shigar da karar a 2015, Saraki ke cewa siyasa ce kawai, kuma an shigar da karar ne saboda ya zamo shugaban majalisa na dole ga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.

A sanarwar da ya fitar bayan wanke Saraki da kotu ta yi, shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da yadda shugaban majalisar dattawan ya jure wa bin matakan shari’a har zuwa lokacin da kotu ta tabbatar da ba ya da laifi.

  • Hukuncin kotu: Shin Saraki ya sha ke nan?
  • Ko ruwa ko zafi muna tare da Saraki – Kwara APC

Yayin da yake sanar da Saraki a matsayin Wazirin Ilori, Sarkin Ilori Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya ce hakan ya tabbatar da amincewarsu ga sha’awar Saraki na kawo ci gaba da gudunmuwa ga Kwara gaba daya ba wai ga masarautar ba kawai.

Sarkin ya kuma ce yana alfahari da Saraki tare da yaba ma tsarin siyasarsa inda ya ce ” ta daga darajar jihar Kwara, musamman masarautar Ilori.”

“A nan muka yi maka addu’ar zama gwamna, da sanata kuma a nan muka yi addu’ar ka zama shugaban majalisar dattawa kuma duka sun tabbata, yau kuma muna addu’ar Allah ya kara daga darajarka daga matsayin da kake a yanzu.” in ji Sarkin Ilori.

Saraki ya bayyana farin cikinsa da godiya ga Allah ga ci gaban da ya samu a masarautar Ilori inda ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, abin ya zo ma sa ba zata.

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *