Boko Haram ta yi wa sojin Najeriya kwanton bauna a Yobe

Taswirar Najeriya

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa sojojin Najeriya harin kwantar bauna a jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabashi.

A sanarwar da ta fitar, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce sojojinta sun kashe ‘yan Boko Haram da dama amma kuma an kashe wasu daga cikin sojojin a musayar wutar da suka yi da mayakan.

Boko Haram ta yi wa sojojin kwanton bauna ne a Babban Gida a ranar Asabar, garin da ba ya da nisa da sansanin sojojin da aka taba kai wa hari a jihar Yobe.

Akalla sojoji 28 aka ruwaito an kashe a harin da aka kai a sansanin inda kuma mayakan na Boko Haram suka kwashi makamai. Amma rundunar sojin ta musanta cewa an kashe jami’anta a harin.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin Texas Chukwu ya aike wa manema labarai ta ce mayakan sun yi wa sojin kwantar bauna ne bayan sun shigo Babban gida domin neman abinci.

Sanarwar ta ce duk da an kashe jami’anta amma ta ci karfin mayakan na Boko Haram kuma yanzu kura ta lafa.

Rundunar sojin ba ta bayyana adadin sojojin da aka kashe ba da kuma adadin mayakan Boko Haram da ta ce ta kashe.

  • Rikicin Boko Haram ya wuce – Buhari
  • Sojin Najeriya sun saki ‘yaran Boko Haram’ 183

A daya bangaren kuma Boko Haram ta kai hari Chadi kusa da kan iyaka inda rahotanni suka ce mutane akalla 18 aka kashe a harin da aka kai a kudancin Daboua.

Mayakan sun yi wa mutane da dama yankan rago tare da yin awon gaba da mata guda 10.

Wannan shi ne hari na uku da aka kai a kasa da mako biyu.

Gwamnatin Najeriya dai ta dade tana ikirarin ta ci galabar Boko Haram, amma wadannan hare haren sun nuna har yanzu Boko Haram barazana ce a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *