Sojoji Sun Samu Fatattakar ‘Yan Boko Haram Da Suka Yi Masu Kwantar Bauna A Sasawa

Rundunar Sojan Nijeriya ta tabbatar da cewa dakarunta sun samu nasarar fatattakar wasu mayakan Boko Haram wadanda suka yi masa kwantar bauna a yankin Sasawa da ke karamar hukumar Babbangida a jihar Yobe.

Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu ya ce, sojojin sun kashe mayakan Boko Haram din da dama inda ya nuna cewa ‘yan Boko Haram din sun yi niyyar kai farmaki kasuwar Babbangida ne da nufin satar abinci tare kuma da kai hari kan sojojin da ke sintiri a yankin. Ya kara da cewa an kashe tare da raunana wasu sojoji a yayin arangamar.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *