Na Bar Jam’iyyar APC Ne, Domin Na Samu Sukunin Aiwatar Da Wasu Abubuwa A Rayuwata – Shehu ABG

 

Tsohon Dan majalisar dokokin tarayya Nijeriya mai wakiltar karamar hukumar Kaduna ta Arewa Alhaji Shehu Usman Bawa wanda aka fi sani da suna Shehu ABG, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC, jam’iyyar da ya kasance cikin jiga jigan da suka kafa ta a jihar Kaduna.

Shehu ABG ya bayyana haka ne a cikin wata takardar sanarwa da ya sanya wa hannu, sannan ya aike da ita ga ofishin jam’iyyar APC na jihar a litinin din nan.

Tsohon Dan majalisar dokokin tarayya wanda ya wakilci karamar hukumar kaduna ta Arewa daga shekarar 2011 zuwa 2015, yace ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne domin kashin kanshi saboda ya samu damar aiwatar da wasu abubuwa na cigaban rayuwar shi.

Shehu ABG wanda yake matsayin mataimaki na musanman ga shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya godewa shugabannin jam’iyyar na jihar Kaduna da sauran ‘ya’yan jam’iyyar bisa ga damar da suka bashi a baya, inda yayi fatan alkhairi ga kowa da kowa.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *