Abubuwa goma da ya kamata ku sani game da Kayode Fayemi

Fayẹmi ati BuhariHakkin mallakar hoto@KFAYEMI
Image captionFayemi ya taka rawar gani a yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015

John Olukayọde Fayemi wanda ya yi takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC shi ne wanda hukumar INEC ta ayyana a matsayin sabon gwamnanjihar Ekiti.

 • An haifi John Olukayode Fayemi ranar tara ga watan Fabraitu na shekarar 1965 a garin Iṣan- Ekiti,da ke karamar hukumar Oye Ekiti ta jihar Ekiti.
 • Ya halarci makarantar Christs’School a garin Ado Ekiti tsakanin shekarar 1975 zuwa 1980.
 • Ya yi karatu a bangaren tarihi da harkokin diflomasiyya a jami’ar Legas da ta Ife (OAU).
 • Ya kuma yi karatun digirin digirgir kan yaki a King’s Collegeda ke jami’ar Landan a Ingila Ọba.
 • APC ta lashe zaben Ekiti
 • Ekiti: ‘Yan sanda sun sa Ayodele Fayose ‘kuka’
 • John Kayode Fayemi ya yi bautar kasa a makarantar ‘yan sanda da ke Sokotoa arewacin Najeriya.
 • Ya yi aikin koyarwa a nahiyar Afirka da Turai da kuma Asiya
 • Haka kuma yi aiki a matsayin malami mai ziyara a kan harkar tsaro kan kasashen bakar fata a jami’ar tsaro taNational Defense University, a Amurka.
Kayọde FayẹmiHakkin mallakar hotoKAYỌDE FAYẸMI/FACEBOOK
Image captionFayemi ya yi ministan ma’adinai a gwamnatin shugaba Buhari daga shekarar 2016 zuwa 2018
 • Ya kasance mai bayar da shawara na musamman ga kwamitin bincike da sasantawa kan tauye hakkin bil Adama da aka yi wa lakabi da Oputa Panel wanda gwamnatin Olusegun Obasanjota kirkiro a shekarar 1999.
 • Ya yi aiki da ma’akatu kamar Africa Research and information Bureau nLandatsakanin shekara1991 zuwa 1993; Deptford City Challeng, aLandaa shekarar 1993 zuwa 1995
 • Ya tab zama gwamnan jihar Ekiti shekarar 2010zuwa, bayan hakan ne kuma ya yi ministan ma’adinai a gwamnatin shugaba Buhari daga shekarar 2016 zuwa 2018 . BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *