Bangaren su Shehu Sani ya fice daga APC

Nasir el-RufaiHakkin mallakar hotoFACEBOOK/GOVERNOR OF KADUNA STATE
Image captionBangarorin biyu ba sa ga-maciji da Gwamna Nasir el-Rufai

Bangarori biyu na jam’iyyar APC a jihar Kaduna wato Akida da kuma ‘yan Restoration sun bayyana ficewarsu daga jam’iyyar a ranar Juma’a.

Sun bayyana hakan ne a lokacin wani taro da bangarori biyu, wadanda suke samun goyon bayan ‘yan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani da Suleiman Hukunyi, suka yi a birnin Kaduna.

Har ila yau ‘yan siyasar wadanda ba sa jituwa da gwamnatin jihar, sun bayyana “yanke kauna da kuma dukkan wata alaka da jam’iyyar.”

Sai dai ba su bayyana jam’iyyar da za su koma ba tukunna.

Shehu SaniHakkin mallakar hotoFACEBOOK
Image captionShehu Sani da Sanata Hunkuyi sun yi dade suna rigima da Gwamna El-Rufa’i

Amma Sanata Shehu Sani da Sanata Hunkuyi ba su halarci taron ba.

Wani jigo a bangaren da suka fice, Mataimaki Tom Mai Yashi, ya shida wa BBC cewa “mun dauki matsayar ne bayan mun tattauna da dukkan mambobinmu. Mun bar jam’iyyar APC har abada.”

Sai dai bangaren uwar jam’iyyar a jihar ya mayar da martanin cewa ‘yan siyasar sun yi hakan ne ba domin bukatun al’ummarsu ba, sai domin biyan bukatun kansu.

  • El-Rufai ya tsine wa sanatocin Kaduna
  • Shin Bola Tinubu zai iya sasanta rikicin APC?
  • Ina shawara kan makomata a APC – Tambuwal

An dade ana kai ruwa rana tsakanin bangaren Gwamnan Jihar Nasir el-Rufai da sauran jiga-jigan ‘yan siyasar jihar.

A makon jiya ne wadansu tsoffin ‘yan sabuwar PDP suka kirkiro wani bangare a cikin jam’iyyar mai mulkin, da sunan Reformed APC, ko rAPC, inda suka bayyana Injiniya Buba Galadima a matsayin shugabansu.

Ana yawan samun takun-saka tsakanin wadanda suka shigo jam’iyyar kafin zaben 2015 da ake kira ‘yan sabuwar PDP da kuma bangaren gwamnatin APC.

‘Yan sabuwar PDP sun yi zargin cewa ba a damawa da su a gwamnatin APC tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya bukatunsu ba.

Sannan a wani bangaren kuma ana tafiya ne da sunan jam’iyya daya, amma akwai masu hamayya da juna a APC musamman a jihohi da dama da jam’iyyar ke mulki.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *