PDP ta yi kawance da jam’iyyu 40 ‘don kayar da Buhari’

AtikuHakkin mallakar hotoTWITTER/PDP

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta kulla wani sabon kawance da wadansu jam’iyyu fiye da 40 da ke kasar, gabanin babban zaben shekarar 2019.

Jam’iyyun sun sanar da hakan ne lokacin wani taro da suka yi a Abuja ranar Litinin, inda suka yi wa kawance lakabi da Coalition of United Political Parties (CUPP).

Sanarwar ta biyo bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya da suka cimma da shugabannin jam’iyyun,”don kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019,” a cewarsu.

Yarjejeniyar ta kunshi wani shiri ta yadda za su tsayar da dan takara daya tilo a zaben shugaban kasa, da na gwamnoni a jihohi da kuma kujerun majalisa.

Sai dai zuwa yanzu jam’iyya mai mulki ta APC ba ta mayar da martani ba, game da batun.

Cikin wadanda suka halarci taron har da shugaban sabuwar jam’iyyar APC Injiniya Buba Galadima da kuma mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu da sauransu.

A shekarar 2015 ne jam’iyyar APC ta doke PDP a babban zaben kasar, bayan ta shafe shekara 16 tana mulkin kasar.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *