PSG na son Coutinho, Madrid ta matsa kan Hazard, ina Ozil zai koma?

Philippe CoutinhoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Paris St-Germain na neman sayen dan wasan Barcelona Philippe Coutinho, mai shekara 26, kan fam miliyan 239, domin hakan ya taimaka wurin shawo kan Neymar ya ci gaba da zama a kulob din, kamar yadda jaridar Mundo Deportivo ta rawaito.

Wasu rahotannin kuma na cewa Neymar, mai shekara 26, na son ganin Edinson Cavani ya bar PSG, inda ake ganin akwai yiwuwar dan wasan gaban na Uruguay ya koma Napolia cewar (Sport).

Manyan ‘yan wasan biyu sun samu sabani a kakar da ta gabata kan neman iko a kulob din.

Shugaban Real Madrid Florentino Perez tuni ya warewa Eden Hazard jesi da lambar da zai saka idan har dan kwallon mai shekara 27 na Chelsea da Belgium ya koma Bernabau da murza-leda, kamar yadda Diario Gol ta rawaito.

Dan uwan Antonio Conte ya bayyana alamun da ke nuna cewa kocin dan kasar Italiya zai ci gaba da zama a Chelsea, a daidai lokacin da ake nuna rashin tabbas kan makomarsa, a cewar Daily Mirror.

Riyad MahrezHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Manchester City ta amince ta biya fan miliyan 60 domin sayen dan wasan gaba na Leicester Riyad Mahrez, mai shekara 27, kuma ana sa ran za a gwada lafiyar dan kwallon na Algeria nan da sa’a 48, kamar yadda jaridar Daily Mail ta rawaito.

Arsenal na tattaunawa da Lorient domin sayen dan kwallon Faransa mai shekara 19 Matteo Guendouzi, a cewar (Sky Sports).

Matteo Guendouzi

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *