Ba za mu ba Fulani makiyaya wurin kiwo ba – Gwamnoinin Kudu maso Gabas

ShannuHakkin mallakar hotoDAILYTRUST
Image captionGwamnonin sun ce ba su da isashen fili a yankinsu

Gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yi shellar cewa babu wata jiha a yankin da za ta ba gwmnatin tarayya fili da za a yi amfani da shi karkashin shirin samar wa Fulani makiyaya wurin kiwo.

Bayan kammala taron da gwamnonin yankin suka yi a karshen makone a fadar gwamnati jihar Enugu, jagoran gwamnonin, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya ce ba za su gwamnati tarayya fili ba saboda ba su da isashen fili a yankinsu.

“Ba mu da isashen fili da za mu ba al’ummarmu balantana kiwo,” in ji shi.

Sai dai gwamnonin sun ce duk da cewa gwamnatin tarayya ba ta nemi fili daga wurinsu ba, amma Mista Umahi ya ce gwamnanonin yanki ba za su amince da bukatarta ba, ko da ta nemi su yi hakan nan gaba.

“Babu filin da za a ba da a yankin kudu maso gashin Najeriya domin kiwon shanu da dabobbi. Babu filin da muka ba da; Ba a bukace mu mu ba da fili ba, kuma ba za mu ba da fili ba.”

“Gwamnonin kudu maso gabashi Najeriya ba su amince a ba da filin domin kiwo a yankin,” in ji shi.

Har ila yau gwamnonin sun ce sun lura da cewa ana fuskantar kalubale game da kiwon da Fulani makiyaya suke yi daga wata jiha zuwa wani yanki “kuma abu ne da ke sanadiyyar barkewar tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya.”

Zebus cattle search for pasture on May 29, 2010.Hakkin mallakar hotoAFP

Gwamnonin yankin sun ce sun kashe makudan kudi wajen biyan manoma diyya saboda barnar da “shanun makiyaya suka yi musu”.

Saboda haka ne gwamnonin suka nemi gudanar da taron gaggawa tare da shugabannin jami’an tsaron kasar.

Rahotanni sun ce gwamnonin jihohin Enugu da Ebonyi ne kawai suka halarci taron, yayin da mataimakin gwamnan jihar Abia da kuma Anambra suka wakilci gwamnoninsu.

Kodayake Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo bai halarci taron ba, hakazalika shi ma mataimakinsa wanda ba sa ga maciji da shi, shi ma bai je taron ba.

Gwamna Okorocha shi kadai ne gwamnan yankin da ke jam’iyyar APC mai mulki.

A kwanakin baya ne majalisar koli kan tattalin arzikin kasar ta yi shellar cewa jihohi 10 a kasar sun amince su ba da filin da za a yi amfani da shi a matsayin wuraren kiwo ga makiyaya da dabobbinsu don kawo karshe rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Duk da cewa gwamnonin yankin kudu maso gabashi mambobi ne a taron majalisar kolin, amma sun ce su ba sa goyon bayan matakin.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *