Cogen NYSC: Kemi Adeosun tana tsaka mai wuya

Kemi AdeosunHakkin mallakar hotoAFP
Image captionKemi Adeosun, wadda ta rantse da Bible lokacin da ta kama aiki, har yanzu ba ta ce uffan ba game da zargin da aka yi mata

Jama’a da dama a Najeriya na ci gaba da kira ga ministar kudin kasar ta yi murabus ko kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya kore ta bayan da aka zarge ta da amfani da takardar shaidar hidimar kasa (NYSC) ta boge domin samun damar yin aiki a kasar.

Jaridar Premium Times ta ce ta bankado yadda Kemi Adeosun ta ki halartar aikin hidimar kasa bayan kammala karatunta a Birtaniya 1989, amma daga bisani ta mallaki takardar “jabu” da ke nuna cewa an dauke mata yin hidimar.

Lamarin, wanda kawo yanzu ministar da ma gwamnatin kasar ba su ce uffan a kai ba, na ci gaba da jan hankalin masu lura da al’amura da ma sauran ‘yan kasar, musamman a shafukan sada zumunta.

Da dama daga cikin wadanda suka yi tsokaci kan batun na yin Allah-wadai da yadda hukumomi suka kasa gano wannan cogen da ake zargin ministar ta yi kafin a nada ta, da kuma yadda kawo yanzu gwamnatin APC da ke ikirarin kawo sauyi ta yi biris da lamarin.

Wajibi ne duk dan Najeriyar da ya kammala karatun digiri ko HND kafin ya/ta cika shekara 30 ya yi aikin hidimar kasa na shekara guda.

Kuma yawancin ma’aikatun kasar ba sa daukar mutum aiki idan ba ya da wannan shaidar.

Yadda labarin ya fito

Dan jaridar Premium Times Abdul’aziz Abdul’aziz ne ya bankado labarin, inda ya bi kwakwaf domin gano inganci ko sahihancin takardun da ministar ta gabatar da ke nuna cewa an dauke mata halartar aikin hidimar kasar.

Bayan binciken ne kuma, wanda ya dauki lokaci ana gudanarwa, jaridar ta ce ta gano cewa shaidar da Misis Adeosun ta gabatar ta boge ce.

Bayan kammala karatunta a shekarar 1989, tana da shekara 22 da haihuwa a Polytechnic of East London.

Ya kamata a ce Misis Adeosun ta zo Najeriya domin yin aikin hidimar kasa, amma sai ta ki yin hakan, inda ta fara aiki a Birtaniya.

Kemi AdeosunHakkin mallakar hotoOTHER
Image captionKemi Adeosun na fuskantar matsin lamba daga sassa daban-daban

Ta yi ayyuka da dama da suka shafi fannin tsumi da tattalin arziki wanda shi ta karanta a jami’a.

Ta koma Najeriya a shekarar 2002, amma duk da haka ba ta je ta halacci NYSC ba, sai kawai ta ci gaba da aiki a wani kamfani mai zaman kansa mai suna, Chapel Hill Denham, kamar yadda Premium Times ta bayyana.

Kwatsam a shekarar 2009 sai ta yanke shawarar karbar takardar shaidar boge wacce ta nuna cewa an amince ka da ta halacci aikin hidimar kasar, a cewar Premium Times.

Tsarin hukumar NYSC ya nuna cewa ba a bai wa duk mutumin da ya kammala makaranta yana/tana kasa da shekara 30 (kamar Misis Adeosun) damar kin halattar hidimar kasa.

Wasu jami’ai a hukumar da ba su amince a bayyana sunansu ba, sun shaida wa jaridar cewa shaidar da ta bayar ta boge ce, domin daraktan da ya sanya wa takardar hannu ya mutu watanni takwas kafin a bayar da takardar ta ta.

BBC ta yi yunkurin jin ta bakin ministar amma mai magana da yawunta Oluyinka Akintunde bai dauki wayarmu ba, kuma bai bayar da amsar sakon da aika masa a rubuce ba.

Mai magana da yawun Shugaba Buhari Malam Garba Shehu, ya shaida wa wakilinmu cewa kamata ya yi “a ji ta bakin ministar tukunna kafin a zo kanmu”.

 • Buhari zai iya yaƙi da cin hanci a cikin gidansa?
 • Buhari ya ayyana dokar ta-baci kan yaki da cin-hanci
 • Hukuncin kotu: Shin Bukola Saraki ya sha ke nan?
Presentational grey line

Tarihin karatun Kemi Adeosun

Buhari da AdeosunHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionShugaba Muhammadu Buhari ne ya nada Mrs Adeosun ministar kudi a 2015, kuma shi ya rantsar da ita
 • An haife ta a shekarar 1967
 • Ta yi digiri a makarantar Polytechnic of East London
 • Makarantar ta sauya suna zuwa University of East London a 1992
 • Ta yi aiki a kamfanoni da dama a Birtaniya
 • Ta dawo Najeriya a 2002, inda ta fara aiki da Chapel Hill Denham

Manyan ayyukan da ta yi

Duk da cewa tana amfani da takardar shaidar “jabu” Misis Adeosun ta ci gaba da aiki a Najeriya, inda ta rike manyan mukamai.

 • Quo Vadis Partnerships – manajan darakta
 • Kwamishinar kudi ta jihar Ogun
 • Ministar kudi ta gwamnatin Najeriya
Presentational grey line

Ra’ayoyin mutane

Jama’a da dama na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan abin da ya faru, kuma mafi yawan mutanen na Allah-wadai da abin da ake zargin ta yi ne.

“@farooqkperogi babbar matsalar a nan ita ce ba wai rashin halartar bautar kasa ba, illa dai kawai amfani da shaidar boge wanda babban laifi ne a dokar Najeriya”.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *