Ko ruwa ko zafi muna tare da Saraki – Kwara APC

Bukola SarakiHakkin mallakar hoto@SPNIGERIA
Image captionReshen APC a Kwara ya ce hadin kan jam’iyyar ya tarwatse

Jam’iyyar APC reshen jihar Kwara ta ce ba za ta taba juya wa shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki baya ba.

Shugaban jam’iyyar na kwara ne Ishola Fulani ya fadi haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda yake bayyana cikakken goyon baya ga Saraki.

“Muna so mu sake jaddada cikakken goyon bayanmu ga jagorancin shugaban majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki, komi ruwa komi zafi muna bayansa”, in ji shugaban jam’iyyar ta APC a Kwara.

Ya kara da cewa: “Mun yi imanin da cewa hadin kai a APC yanzu ya yi rauni, ya tarwatse kuma yanke”.

Wannan na zuwa bayan kotun koli ta wanke Sanata Saraki daga tuhumarsa da aka yi yin karya wajen bayyana kadarorinsa, karar da gwamnatin Buhari ta APC ta shigar a gaban kotu.

Tun shigar da karar a 2015, Saraki ke cewa siyasa ce kawai, kuma an shigar da karar ne saboda ya zamo shugaban majalisa na dole ga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.

Shugaban jam’iyyar reshen Kwara, Mista Fulani ya ce, “muna farin ciki da hukuncin da ya kara tabbatar da shugaban majalisar Dattawa ba ya da wani laifi.”

Hakan dai ya tabbatar da abin da zai iya biyo wa baya ga makomar APC a jihar Kwara idan har Saraki ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar.

Wanke Saraki da kotu ta yi na zuwa bayan wasu ‘yan sabuwar PDP suka sanar da kirkiro wani bangare a jam’iyyar APC, da sunan R-APC, tare da bayyana Injiniya Buba Galadima a matsayin shugabansu.

Kuma ana ganin Saraki yana daya daga cikin shugabannin da ke jagorantar ‘yan a waren daga uwan jam’iyyarsu ta APC bayan shugabannin taron na R-APC, sun ce da yawun su Saraki da Kwankwaso da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara aka dauki matakin

Bukola SarakiHakkin mallakar hotoFACEBOOK/NIGERIAN SENATE
Image captionHukuncin kotun kolin wanda ba za a iya daukaka kara ba, ya wanke Sanata Saraki daga zarge-zargen da ake ma sa

A kwanan nan ne gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya shaidawa BBC cewa yana nazarin ficewa daga jam’iyyar APC da kuma yiyuwar komawa jam’iyyar PDP.

Kalaman gwamnan na Sakkwato na zuwa bayan daya daga cikin ‘yan sabuwar PDP tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan APC Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yanzu shi ba dan kowace jam’iyya ba ne.

Duk da bai fito ya ce ya fice daga APC ba amma Kwankwaso kuma ya yi ikirarin zai iya doke Shugaba Buhari idan jam’iyyar PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

Rikicin bangarori a APC da kuma barazanar ficewa daga bangaren ‘yan sabuwar PDP ya dada fito da girman kalubalen da ke gaban jam’iyyar kafin zaben 2019.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *