Spain ta kori kocinta Fernando Hierro

Fernando HierroHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionHierro ya fara horar da tawagar Spain saura kwana biyu a soma gasar kofin duniya a Rasha

Spain ta raba gari da Fernando Hierro da ta nada matsayin kocinta kwana biyu a soma gasar cin kofin duniya a Rasha.

Hukumar kwallon Spain ta ce Fernando Hierro ba zai ci gaba da aikin horar da ‘yan wasan kasar ba bayan fitar da kasar daga gasar cin kofin duniya a Rasha.

A bugun fanareti Rasha ta fitar da Spain daga gasar cin kofin duniya a zagaye na biyu.

Hierro wanda tshon kaftin din kasar ne, ba ya da wata kwarewa a aikin horar da ‘yan wasa.

Ya zama kocin Spain ne dab da gasar cin kofin duniya bayan korar Julen Lopetegui saboda yarjejeniyar da ya kulla da Real Madrid.

  • Rasha ta fitar da Spain a fanareti
  • Iniesta ya yi ritaya daga Spain
  • Spain ta kori kocinta Lopetegui

A sanarwar da ta fitar, hukumar kwallon Spain ta ce ta raba gari da Fernando Hierro.

Ta kuma ce Hierro ya ki amincewa ya koma ga tsohon aikinsa kafin nada shi matsayin kocin Spain.

Spain dai ta kori Lopetegui don gudun samun sabani tsakanin tawagar kasar musamman daga bangaren ‘yan wasan Barcelona da Real Madrid bayan sanar da shi a matsayin sabon kocin Madrid.

Spain ta kori Lopetegui ne saura kwana biyu a bude gasar cin kofin duniya a Rasha.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *