Yadda rayuwar Marigayi Adamu Ciroma ta kasance

A ranar Alhamis 6 ga watan Yuli ne Allah ya yi wa fitaccen dan siyasar nan da ya rike manyan mukaman gwamnati da dama a Najeriya, Malam adamu Ciroma rasuwa.

Ya rasu yana da shekara 83 bayan ya sha fama da rashin lafiya a wani asibiyi mai zaman kansa a Abuja, babban birnin kasar.

An yi jana’izarsa a Abujar a ranar da ya rasun da yamma.

Manyan mutane da dama ‘yan kasa a ciki da wajen Najeriyar sun yi aika sakon ta’aziyya ga iyalansa a shafukansu na sada zumunta.

A wata sanarwa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fitar ta hannun mataimakinsa kan harkar watsa labarai Femi Adesina, ya bayyana rasuwar mAdamu Ciroma a matsyain wani babban rashi.

Ya kara da cewa: “Ba za a manta da rayuwar Ciroma da irin ayyukan taimakwa kasa da sadaukarwar da ya yi ba don kawo hadin kai da cigaba.”

Shugaba Buhari ya kuma kara da cewa: “Za a girmama tsohon gwamnan babban bankin saboda irin gudunmowar da ya bayar don ciyar da dimokradiyya gaba kuma abubuwan da za a iya tunada shi za su dinga tunasar da ‘yan siyasa wadanda suke son cigaban al’ummarsu da kasarmu baki daya.”

Wani fitaccen dan jarida mai rubutu na musamman a jaridar Daily Trust Malam Mahmud Jega, ya yabe shi a wani rubutu da ya yi da cewa Malam Adamu Ciroma na da basira da iya tsara magana da kwarewa a aikin jarida da kwarewa a siyasa kuma mai dumbin ilimi ne da bin dokokin addini.

“Halayensa halaye ne da ban gansu tattare da wasu ‘yan Najeriyar da dama ba,” in ji Mahmud Jega.

Presentational grey line

Tarihin Adamu Ciroma

Adamu CiromaHakkin mallakar hotoOTHER
Image captionMarigayin ya rike mukamai da dama a tsawon shekaru a kasar

An haifi Alhaji Adamu Ciroma a watan Nuwambar 1934 a garin Fika da ke karamar hukumar Potiskum a jihar Yobe, arewa maso gabashin Najeriya.

Ya fara karatunsa na firamare a Potiskum sai kuma ya zarce makarantar sakadanrae ta Bornu Middle School da Kwalejin Barewa ta Zariya, da kuma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Zariya.

Malam Adamu Ciroma ya kammala Jami’ar Ibadan a shekarar 1961 ya kuma fara aikin gwamnati.

Malam Ciroma ya zama editan jaridar New Nigerian, kuma shi ne mutum na farko da ya zama editan jaridar tun lokacin da Sir Ahmadu Bello Firimiyan jihar arewa ya kaddamar da ita.

A 1969 kuma ya zama Manajan Darakta na kamfanin jaridar ta New Nigeria.

Malam Ciroma ya bar aiki a kamfanin jaridar a 1974. A lokacin mulkin Janar Murtala Muhammed ne aka nada Malam Adamu Ciroma matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, CBN a shekarar 1975.

Shekara biyu bayan nan sai ya yi murabus daga wannan mukami don tsayawa takara a majalisar tsara kundin mulkin Najeriya na 1979.

Da shi aka kafa jam’iyyar NPN a 1978, kuma ya tsaya takara a karkashinta tare da wasu mutum biyar.

Daga baya ya mara wa Alhaji Shehu Shagari baya. Ya kuma zamo sakataren jam’iyyar na kasa har zuwa shekarar 1979 lokacin da Alhaji Shehu Shagari ya nada shi daya daga cikin ministocinsa.

Presentational grey line

A watan Satumbar 1983 ya zama shugaban kwamitin mika mulki daga wata gwamnatin zuwa wata, da aka dora musu aikin ba da shawarar yadda za a sake fasalta Najeriya.

Sallar jana'izar Adamu CiromaHakkin mallakar hotoTWITTER/@SPNIGERIA
Image captionAn yi wa marigarin sallar jana’iza ne a masallacin Al Noor da ke Abuja ranar Alhamis

A shekarar 1992 ne ya tsaya takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NRC amma sai gwamnatin Ibrahim Babangida ta haramta musu tsayawa takara.

Malam Adamu Ciroma ya yi kaurin suna wajen nuna matukar adawa da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha.

Bayan dawowar mulkin dimokradiyya a Najeriya, Adamu Ciroma na daga cikin jiga-jigan da suka kafa jam’iyyar PDP a shekarar 1998. Su marawa tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo baya inda ya zama shugaban kasa.

Malam Ciroma ya rike mukamin minsitan kudi daga 1999 zuwa 2003.

Haka ma matarsa Maryam Inna Ciroma ta taba rike mukamin ministar mata a mulkin Obasanjo karo na biyu a shekarar 2005. Ta kuma zamo shugabar mata ta kasa ta jam’iyyar PDP.

Ya rasu ya bar mace daya Hajiya Maryam Ciroma da ‘ya’ya uku da kuma jikoki biyar.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *